A karo na uku, daya daga cikin kamfanonin sadarwa da ke Afirka, wato kamfanin sadarwa na Telecom ya kara samar da kayayyakin da zasu bunkasa hanyoyin sadarwarsa da kuma samar da ababen more rayuwa ta hanyar hadin guiwa da YahClick, domin samun damar isar da sako cikin hanzari, musamman ga ‘yan Nijeriya.
Kamfanin ya ce sakamakon hadin guiwar da suka yi, za a samu karin kananan tashoshin watsa shirye-shirye a fadin kasarnan, wadanda zasu dinga gabatar da shirye-shiryensu yadda al’uma zasu samu kyakkyawar fahimta.
- Yawan Tashar Sadarwa Ta 5G Da Sin Ta Gina Ya Kai Kusan Miliyan 2
- An Kaddamar Da Taron Koli Na Raya Fasahar Sadarwar Zamani Na Kasar Sin Karo Na 5
Kamar yadda mataimakin shugaban kamfanin da ke kula da bunkasa hanyoyin sadarwa, wanda kuma shi ne ya kaddamar da wannan tashar kashi na uku, Muhammed Bashir ya ce, “Za a amfana da kananan tashoshin sadarwarmu ta bunkasa harkokin rayuwa da kasuwanci a wannan yanki.
Bashir ya bayyana wannan batu ne a wani sako da ya aika wa manema labarai, sannan kuma ya ce, dangane da hadin guiwa tsakanin Telecom da YahClick.
Wwadanda suke kan gaba a harkar kasuwanci a dukkan fadin Afirika, zai samar da dabaru kasuwanci a tsakanin masu amfani da wannan kamfani a dukkan fadin Nijeriya, yadda za a kawo karshen kalubalen samar da kayakkyawan yanayin kasuwanci.”
Haka kuma a kashi na ukun, shugaban kamfanin Stanley Jegede, ya bayyana cewa, idan aka kara fakaka wakannan tashoshin, za a samu karin nisan zangon isar da shirye-shirye a wasu sassa da ke fadin kasarnan.
Ya ce, kashi na uku ne kan gaba wanda ‘yan kasa suka mallaka a matsayin wata babar hanyar isar da sakonni ta hanyar amfani da netiwok.