• Leadership Hausa
Sunday, August 7, 2022
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Dausayin Musulunci

Sabuwar Shekarar Musulunci Ta 1444: Hikimar Jujjuya Lokaci Da Allah Yake Mana

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
2 days ago
in Dausayin Musulunci
0
Sabuwar Shekarar Musulunci Ta 1444: Hikimar Jujjuya Lokaci Da Allah Yake Mana
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A’uzu billahi minash shaidanir rajim, bismillahir rahmanir Rahim. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim. Masu karatu barkanmu da sake haduwa a wannan makon cikin filinmu na Dausayin Musulunci. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata mun kammala karatun da muke yi a kan falalar ziyarar Kabarin Annabi (SAW). Allah ya amfanar da al’ummar Annabi (SAW) da shi.

A yau kuma za mu shiga sabon karatu a kan sabuwar shekarar Hijirah wadda a bana ita ce ta 1444.

  • Jihar Nasarawa Ta Fadakar Da Al’ummarta A Kan Cutar Hanta
  • Bincikenmu: An Dade Da Hana Karuwanci A Neja, Amma Abin Ya Dau Sabon Salo

Shi Musulmi kullum cikin ganin girman baiwar Allah yake, kullum a cikin kankan da kai yake a wurin Allah, cikin bautar Allah Tabaraka wa ta’ala.

Don haka Allah yake ta jujjuya mana kwanaki da watanni da shekaru domin abin ya ba da sha’awa ya yi kyau. Kuma ya zamto kullum Musulmi ya sabunta himmarsa da tafiyarsa zuwa ga Allah. Yanzu mun gode Allah, mun yi karatuttuka game da Hajji, ga shi har an kammala Hajjin ma, mun gode Allah.

Sannan ita kanta shekarar ma ta kare, mun shiga sabuwar shekara ta 1441 da yin Hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makka zuwa Madina tare da kafa Daular Musulunci. Idan ka kawo shekara 53, sai lissafi ya zama shekara 1494 da haihuwar Annabi (SAW). Mun gode Allah.

Labarai Masu Nasaba

Ziyarar Kabarin Annabi SAW (3)

An Sauya Wa Ka’aba Sabuwar Rigar Da Kudinta Ya Kai Dala $6.5m

Lallai wannan kalanda ana ce mata ta Musulunci; gaskiya ne, ta Musulmi ce tsantsa sannan kuma ta duk halitta ce domi duk halitta suna amfani da wannan, ko sun sani ko ba su sani ba. Sai dai kawai, mu a cikin ibadojinmu Addininmu Balarabe ne kuma Larabawa da wata suke yin kirgensu, kuma shi ne ya dace da halittar Dan Adam, mun gode Allah.

Annabi (SAW) ya umurce mu mu bi sunnarsa, mu bi sunnar Khalifofi shiryayyu bayansa.

Wannan Hijirah sunnar Manzon Allah (SAW) ce. Kuma sunnar Sayyidina Umar ce (RA) da sauran Sahabbai. Domin Sayyidina Umar ne ya kafa mana wannan kalandar ko in ce kirgen ta Hijirah.

Manzon Allah (SAW) ya yi Hijira ne a watan Rabi’ul Auwal, amma me ya sa ba a faro kirgen daga watan ba? Abin da suka yi na farowa daga Muharram akwai kaifin hankali a ciki.

Akwai watababbar hidima a cikin watan na Rabi’ul Auwal, ita ce murnar haihuwar Manzon Allah (SAW).

Idan abu biyu ya zamo wuri daya sai daya ya kwace daya, kamar a ce yau ce ranar haihuwar Manzon Allah kuma yau ce ake bikin sabuwar shekarar Hijira, dole daya ya kwace daya.

Bare wanda aka hada da shin ma Mauludi ne na Manzon Allah (SAW). To, shin waye ana bikin haihuwar Manzon Allah zai tuna ya yi wata murnar sabuwar shekara? Wannan ya sa suka dauko farawar sabuwar shekarar suka matso da ita baya ta fara a watan Muharram.

Sannan a halittar Allah, Allah ya shirya cewa wata guda 12 ne, idan wata ya fito ya koma a ce Muharram, idan ya fito ya yi girma har ya cika kuma ya fara karewa har ya tafi baki daya sai a ce Muharram ya kare, idan ya kuma fitowa sai a ce Safar. Watan da ya fito a Muharram shi din ne dai zai kara fitowa bayan karewarsa a Muharram din a ce Safar.

Shi din ne dai yake ta wannan juyawar. To watan idan zai yi ta fitowa babu kayyadadden kirga, sai a yi ta kirgawa har zuwa miliyoyi.

Shi ya sa Allah ya shirya cewa idan watan ya fito sai a ce daya, idan ya koma ya sake fitowa a ce biyu har dai a yi 12. Idan an yi haka sai a ce shekara ta kare, sai a kuma dawowa wata sabuwar shekara.

To a wannan abu da Allah ya shirya, sai ya sanya Almuharram a matsayin farkon wata. La’alla Annabi Adamu (AS) yana da wani suna da yake kiran watan daban da na Larabawa ko kuma ya zama daya ne, ga shi nan dai Muharram shi ne farko.

Wanda aka gada wajen Larabawa dai Almuharram shi ne farko, sai Safar, Rabi’u Auwal, Rabi’u Akhiri, Jimada Auwal, Jimada Akhir, Rajab, Sha’aban, Ramadan, Shauwal, Zul Kida sai kuma Zul Hajji.

Sauran wasu Yarukan ma suna da nasu, kamar Turawa suna da Janairu, Fabarairu, Maris har zuwa Disamba.

Idan ka ce ai na turawan sunayen gumaka ne, to ai na Musuluncin ma ba sunayen Allah ne aka sa musu ba, kinaya ce. Kila an ambace su da yanayin da ake samu a lokacinsu.

Kila kamar lokaci ya yi zafi akwai rana sosai sai a ambace shi da Ramadana, idan kuma Rajab ne kila lokacin da suke cire kan mashi ne saboda ba za a yi yaki ba, sai a ce masa Rajab.

Ko wanne dai za ka ga kila saboda wani abu da yake faruwa lokacin aka ambaci watan da sunansa na wannan abun. To amma Annabi (SAW) lokacin Hajjinsa na karshe a cikin hudubarsa ya fadi cewa, “zamani ya kewaya ya kewayo”.

Tun ranar da Allah ya halicce shi a Azal, aka fara da Muharram a farko, haka abin yake har zuwa 12. Sai dai, ko wane yaruka suna da nasu.

Yanzu lokacin da wannan Muharram din ya shiga, ya kasance a karshen wata na 7 ne a wurinsu. Su dai suka kai shi na 7 mu babu ruwanmu, a wurin Allah dai Muharram shi ne na daya.

Don haka idan Musulunci zai yi kirge dole ya dawo Muharram, bai taba na Rumawa da sauransu ba saboda ba za su yarda ba.

Wannan shi ne dalilin da ya sa ba a sa Rabi’u Auwal a matsayin farkon watan shekarar Musulunci ba, da kuma kasancewar Rabi’ul Auwal shi ne na uku a watannin Musulunci, kuma ai ba za a fara kirge daga uku ba.

Wannan ya sa Rabi’ul Auwal bai zama farkon shekara ba. Haka Allah ya shirya tun Azal.

Haka Annabi (SAW) ya fada a ranar Hajjin ban-kwana cewa zamani ya kewaya ya kewayo.

Ka ga yanzu, Allah ya ganar da Sahabbai abin da Annabi (SAW) ya koyar da su, kuma dama mutane ne Malamai, duk abin da Annabi (SAW) ya koyar da su suna yi a aikace.

Sannan me ya sa ba za mu dinga yin murnar shekarar ba a watan da aka yi Hijirar na Rabi’ul Auwal? Sai mu ce watan Rabi’ul Auwal yana da nashi gagarumin murnar da muke yi na bikin haihuwar Manzon Allah (SAW), shi kenan ka ga ba sai an rungumi wani biki na daban an sake kaiwa cikinsa ba.

Kalmar dai yadda aka samu sabani na ilimi a tsakanin Sayyidina Umar da Sayyidina Aliyu (RA). Domin sabanin malamai rahama ne ga al’umma.

Za mu tsaya a nan sai mako mai zuwa za mu ci gaba cikin yardar Allah. Allah ya kaimu da rai da lafiya Albarkar Annabi (SAW).

Tags: Allah SWAKalandar MusulunciManzon Allah SAWSabuwar Shekarar Musulunci
ShareTweetSendShare
Previous Post

An Kulla Yarjejeniyar Kasuwanci Tsakanin Kamfanonin Sadarwa Na Telecom Da YahClick

Next Post

Yaje-Yajen Aiki Na Neman Yi Wa Gwamnatin Buhari Katutu 

Related

Ziyarar Kabarin Annabi SAW (2)
Dausayin Musulunci

Ziyarar Kabarin Annabi SAW (3)

1 week ago
An Sauya Wa Ka’aba Sabuwar Rigar Da Kudinta Ya Kai Dala $6.5m
Dausayin Musulunci

An Sauya Wa Ka’aba Sabuwar Rigar Da Kudinta Ya Kai Dala $6.5m

1 week ago
Ziyarar Kabarin Annabi SAW (2)
Dausayin Musulunci

Ziyarar Kabarin Annabi SAW (2)

2 weeks ago
Zaben Osun: Yadda Mawaki Portable Ya Sha Suka Kan Goyon Bayan APC
Dausayin Musulunci

Zaben Osun: Yadda Mawaki Portable Ya Sha Suka Kan Goyon Bayan APC

3 weeks ago
Abubuwan Da Aka Halatta Da Wadanda Aka Haramta Ga Mahajjaci (II)
Dausayin Musulunci

Ziyarar Kabarin Annabi (SAW) 1

3 weeks ago
Arfa
Dausayin Musulunci

Garabasa Da Falalar Tsayuwar Arfa

4 weeks ago
Next Post
Yaje-Yajen Aiki Na Neman Yi Wa Gwamnatin Buhari Katutu 

Yaje-Yajen Aiki Na Neman Yi Wa Gwamnatin Buhari Katutu 

LABARAI MASU NASABA

Peter Obi Ba Zaiyi Nasarar Lashe Koda Rabin Jihar Nasarawa Ba – Inji Deji Adeyanju

Peter Obi Ba Zaiyi Nasarar Lashe Koda Rabin Jihar Nasarawa Ba – Inji Deji Adeyanju

August 7, 2022
Hukumar NIS Ta Cafke Masu Safaran Makamai 3 A Kurus Ribas

Hukumar NIS Ta Cafke Masu Safaran Makamai 3 A Kurus Ribas

August 7, 2022
MDD Da Gwamnatocin Kasashe Daban-Daban Sun Sake Jaddada Tsayawa Ga Manufar Kasancewar Kasar Sin Daya Tak A Duniya

MDD Da Gwamnatocin Kasashe Daban-Daban Sun Sake Jaddada Tsayawa Ga Manufar Kasancewar Kasar Sin Daya Tak A Duniya

August 7, 2022
Naira Miliyan 5 Nake Nema Don Fansar Mahaifiyata – Mace Mai Safarar Kwayoyi

Naira Miliyan 5 Nake Nema Don Fansar Mahaifiyata – Mace Mai Safarar Kwayoyi

August 7, 2022
Wakilin Sin Ya Ki Amincewa Da Zargin Da Amurka Ta Yi Kan Manufofin Makamashin Nukiliyar Kasar Sin

Wakilin Sin Ya Ki Amincewa Da Zargin Da Amurka Ta Yi Kan Manufofin Makamashin Nukiliyar Kasar Sin

August 7, 2022
NDLEA Ta Cafke Tsohon Sojan Da Ke Wa ‘Yan Bindiga Safarar Miyagun Kwayoyi

NDLEA Ta Cafke Tsohon Sojan Da Ke Wa ‘Yan Bindiga Safarar Miyagun Kwayoyi

August 7, 2022
Sharhi: Yadda Kasar Amurka Ta Nuna Fuska Biyu A Kan Batun Taiwan

Sharhi: Yadda Kasar Amurka Ta Nuna Fuska Biyu A Kan Batun Taiwan

August 7, 2022
Matsalar Tsaro: An Gudanar Da Addi’oi Na Musamman A Yankin Funtuwa

Matsalar Tsaro: An Gudanar Da Addi’oi Na Musamman A Yankin Funtuwa

August 7, 2022
Cinikayyar Waje Ta Hajojin Sin Ta Bunkasa Da Kaso 10.4 Bisa Dari Cikin Watanni 7 Na Bana

Cinikayyar Waje Ta Hajojin Sin Ta Bunkasa Da Kaso 10.4 Bisa Dari Cikin Watanni 7 Na Bana

August 7, 2022
An Nemi Jam’iyyar APC Ta kara kaimi Wajen Biyan Bukatun ‘Yan Nijeriya

An Nemi Jam’iyyar APC Ta kara kaimi Wajen Biyan Bukatun ‘Yan Nijeriya

August 7, 2022
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.