Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ta bayyana cewa, an kwaso ‘yan Nijeriya dari da bakwai da suka makale a birnin Tripoli na kasar Libya.
Mutanen da suka dawo sun iso kasar nan ne ta jirgin Al Buraq Air Boeing 737-800 mai lamba 5A-DMG wanda ya sauka da misalin karfe 3:55 na rana a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Ikeja a Jihar Legas.
- Da Dumi-Dumi: APC Ta Kori Goje Daga Jam’iyyar Kan Zargin Yi Mata Zagon Kasa
- Gobara Ta Tashi A Wani Sashen Kwalejin Queens Da Ke Jihar Legas
Sun samu tarba daga babban daraktan hukumar NEMA, Mustapha Ahmed, wanda ya samu wakilcin babban jami’in bada agajin gaggawa, Mista Aziz Afunku.
Daga cikin wadanda aka dawo da su akwai jariri maza da mata, yara mata biyar da yara maza uku.
Shugaban NEMA ya bayyana cewa an dawo da ‘yan Nijeriya 105 da suka makale tare da karin wasu 281 da aka dawo da su kasar nan a watan Maris 2023.
A watan Afrilun 2023, ya zuwa yanzu an taimaka wa ‘yan Nijeriya 259 su dawo gida.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM) tare da goyon bayan abokan huldar kasa da kasa ke taimaka wa ‘yan Nijeriya da ke cikin mawuyacin hali da ke makale a kasar Libya domin dawowa gida tun daga shekarar 2017.