Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM) ta kwaso ‘yan Nijeriya 151 da suka makale daga birnin Benghazi na kasar Libya.
Kabiru Musa, mai kula da Ofishin Jakadancin Nijeriya a Libya ne, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a ranar Talata a Abuja.
- Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Azama Wajen Dakile Hadurran Dake Tunkarar Tattalin Arzikin Duniya
- SERAP Ta Nemi INEC Ta Hukunta Gwamnoni Kan Bangar Siyasa
A cewar Musa, wadanda aka kwaso sun hada da mata 71, maza 54, yara 14 da jarirai 13 ana sa ran za su iso filin jirgin na Murtala Mohammed Legas da karfe 8 na dare.
Musa ya ce, a shekarar 2022, ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta IOM ta yi nasarar dawo da ‘yan Nijeriya kusan 4,000 da suka yi hijira ba bisa ka’ida ba a kasar.
“A karkashin shirin na IOM na komawa gida, mun yi nasarar kwashe ‘yan Nijeriya 151 da suka makale daga birnin Benghazi zuwa Legas, Nijeriya da misalin karfe 16:00 na safe a cikin jirgin haya mai lamba. UZ189.
“Ana sa ran jirgin zai isa filin jirgin sama na Murtala Mohammed, ds ke Legas da karfe 20:00 na safe agogon Nijeriya a wannan rana.
“Akwai ’yan Nijeriya da dama da ke rayuwa ba bisa ka’ida ba a kasar nan, kuma Gwamnatin Tarayya ta hannun Ofishin Jakadancin a nan, ta ci gaba da shiga tsakani da hukumomin kasar nan don kawo karshen lamarin.
“A ko yaushe akwai jami’an hukumomin gwamnati da suke a kasa don karbar su tare da tabbatar da sake tsugunar da su da kuma dawo da su cikin al’umma,” in ji Musa.
Musa, ya ce za a kwashe wasu ‘yan Nijeriya daga birnin Tripoli a ranar Laraba, tare da gudanar da wani aikin a ranar 3 ga Afrilu daga Misrata na kasar Libya.