Rundunar ‘yansandan Babban Birnin Tarayya ta sanar da kwato murafun manyan kwalabati 125 da aka sace a Abuja, inda ta nuna kudirinta na murkushe masu aikata ayyukan da suka shafi ababen more rayuwa na jama’a.
A Liman, an kwato na baya-bayan nan ne a ranar 4 ga watan Mayun 2025, a yayin da aka samu wasu bayan sirri a yankin Dei-Dei, inda jami’ansu suka gano abubuwan da aka sace kuma aka boye a cikin rami.
Rundunar ‘yansandan ta bayyana cewa, an samu nasarar ne ta hanyar samun bayanai daga wani jami’in ‘yansanda, inda ya bayyana muhimmancin hadin kan jama’a wajen magance miyagun laifuka.
- ‘Yansanda Sun Kubutar Da Wata Mata Da Aka Yi Garkuwa Da Ita A Otal Din Abuja
- ‘Yansanda Sun Kubutar Da Wata Mata Da Aka Yi Garkuwa Da Ita A Otal Din Abuja
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan Babban Birnin Tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya fitar a ranar Lahadi, ta jaddada kudurin rundunar na yaki da satar kayayyakin more rayuwa.
AN ruwaito kwamishinan ‘yansanda, Olatunji Disu yana cewa, “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen neman kadarorin jama’a da aka sace.
“Jami’anmu na kara zage damtse wajen ganowa tare da wargaza ma’ajiya da wuraren ajiya ba bisa ka’ida ba inda ‘yan fashin suka rika tara kayayyakin da aka sace. Dole ne FCT ta kubuta daga hannun wadannan miyagun abubuwa.”
Aikin dai ya biyo bayan nasarar da aka samu a makon da ya gabata inda rundunar tare da hadin gwiwar rundunar hadin gwiwa da ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya kafa, suka kama tare da kwato kayayyakin more rayuwa da aka lalata.
Disu ya yaba wa mazauna yankin bisa ci gaba da ba su goyon baya, ya kuma bukace su da su kasance cikin taka tsan-tsan, yana mai jaddada cewa kare kadarorin jama’a wani nauyi ne da ya rataya a wuyansu.
Umurnin ya kuma karfafa wa mazauna yankin da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi ta hanyar amfani da lambobin tuntubar gaggawa.