Daga Abubakar Abba,
Wata tsohuwar ‘yar takarar majalisar dokokin jihar Katsina daga mazabar Funtuwa Hajiya Zainab Abdu Ghana ta koka da cewa, duk girman Jihar Katsina mata biyu ne kacal, su ke wakilci duk miliyoyin matan jihar baki daya.
Hajiya Zainab Abdu Ghana a hirarta da Leadership Ayau ta bayyana cewa, “Mu ba a bamu ba kuma bai wa ba wadanda suka fimu ba, inda ta yi nuni da cewa, da kayi magana sai ace baka da hakuri.”
A cewar Hajiya Zainab Abdu Ghana, saboda Allah ace duk girman Jihar Katsina mata biyu ne za su wakilci duk miliyoyin matan jihar baki daya.
Hajiya Zainab Abdu Ghana ta yi nuni da cewa, “Idan na kalli takwarorina na wasu jihohin wallahi inashan mamaki, inda ta kara da cewa, sannan idan kaje wasu jihohin za ka ga mata wakilan Al’umma masu mukami iri daban-daban gwanin shaawa.”
A cewar Hajiya Zainab Abdu Ghana “Munan sai dai mukamin kungiya wanda kowa ke ba kanshi da kanshi kuma wasu don dole ma sun hakura tunda ko kudin office da suka kama haya basu iya biya. Kada amanta munyi kokari mata fiye da maza, domin kuwa layin mu sai ya ninka na maza awajen zabe.”
Hajiya Zainab Abdu Ghana ta kara da cewa, yanzu haka idan kaga anyi kyautar mota to namiji ne idan kaga anyi kyautar wasu kudade manya to maza ne, inda ta kara da cewa, haka kuma idan wata kwangila za a bayar, maza ake bai wa duk da ance ana bai wa bakin da ko katin zabe ba su da shi.
Ta jaddada cewa, “Mu da muka wahala da iyayen mu da dangin mu wanda mukai masu dole ko da ba su so, mun sa su sunyi, inda ta kara da cewa, duk cikin mu ba mu cancanta aba ko daya ba sai an dauko wasu daga wata jihar an ba su aiki ajihar mu abin takaici.”
Hajiya Zainab Abdu Ghana ta kara da cewa, an mai da matan mu ‘yan bangar siyasa da bin office office suna neman yadda za su ci abinci, alhali mu na da wadanda suka yi karatun Boko da kuma wadanda suka kamata a taimaka wa ta wasu fannoni don suma su taimaki kansu da ‘yan’uwansu.
Ta bayyana cewa, “Na yi mamaki da wasu mata suka kirani a waya suka ce, wallahi na manta da su domin kuwa lokacin da ake gwagwarmaya tare muke fadi tashi da su, inda suka ce min, anci moriyar ganga an yard a kwaure.”
Ta kara da cewa, wasu kuma sun ce min, Zainab Ghana an shige Gwamnati anyi shiru ba a ko neman mu kuma ina alkawarin da kikayi mana, inda ta kara da cewa, da suka fara magana har sai da ta kai ga hakuri kawai nake ba su saboda bansan me zance masu ba, kuma komin daren dadewa, in dai ana siyasa dole an neme su bayan ba su san cewa, nima basu san ko godiya ba a yi mani ba.