Hukumar Gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha da ke Kano ta nada mataimakin shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayyar da ke Dutsima a jihar Katsina, (FUDMA) Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi, a matsayin mamba.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Jami’ar (FUDMA) Kwamared Habibu Umar Amin, ya sanya wa hannu ya raba wa manema labarai a Katsina.
- Bana Satar Mutane, Kashe Su Kawai Nake Yi – Kasurgumin Dan Bindiga, AleiroÂ
- Wayar Da Kai: INEC Za Ta Hada Hannu Da Kungiyar ‘Darika Awareness Forum Katsina’Â
Haka kuma sanarwa ta ce nadin Farfesa Bichi, ya zo ne bayan amincewar hukumar gudanarwa ta MAAUN bayan kammala wani taro da ta yi a ranar 25 ga Fabrairu, 2022 a jihar Kano.
Da yake taya Farfesa Bichi murna, shugaba kuma wanda ya asasa Jami’ar Maryam Abacha, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya ce zaben Bichi ya biyo bayan dogon nasiri kafin lalubo shi cikin dubu saboda kima da girma da kuma yadda ya sadaukar da kansa wajen ci gaban ilimi da al’umma.
“Zaben da aka yi wa Farfesa Bichi ya kara tabbatar da nagartarsa musamman kokarinsa wanda ya zama misali a kan ba da tallafin karatu ga dalibai, saboda haka ina kara taya ka murna” in ji Gwarzo.