Hukumar Hisbah a Jihar Katsina ta yi garanbawul a shugabancinta a matakin jiha tare da maye gurbin wasu sabbin shugabanni.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata samarwa da sakataren hukumar, ya fitar aka raba wa manema labarai a Katsina.
- An Gurfanar Da Wani Mutum A Kotu Kan Satar Dan Bunsuru 2
- Abba Gida-Gida Ya Karbi Shaidar Lashe Zaben Gwamnan Kano
Sanarwar, ta ce tana sanar da al’umma game da wasu sauye-sauye da a ka samu a shugabancin Hisbah da suka shafi ofishin kwamandan jiha da magatakarda da kwamandan ladabtarwa da sauransu.
Hukumar ta ce ta maye gurbin tsohon kwamandan da Muhammad Rabi’u Garba, sai Abdullahi Yusuf a matsayin mataimakin kwamanda da kuma Muhammad Aminu Bello a matsayin magatakarda
Sauran sun hada da Muhammad Mahdi Rabi’u wanda ya maye gurbin kwamandan ladabtarwa sai kuma Abubakar Iliya a matsayin shugaban da’awa na Jihar Katsina.
Sanarwar ta ci gaba da bayanin cewa ta gode wa tsohon shugabanta na jiha Malam Hamisu Abubakar Imam a kan irin ci gaban da ya kawowa Hisbah a lokacinsa da kuma yi masa fatan nasara a rayuwarsa.
Haka kuma a jawabinsa sabon kwamandan Hisbah na Jihar Katsina, Muhammad Rabi’u Garba ya ba da tabbacin yin aiki tukuru ga al’ummar Jihar Katsina, da kuma kokarin kara bunkasa ayyukan Hisbah zuwa lunguna da sako-sako jihar.
Kazalika, ya taya zababben gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda murnar nasara da ya yi a zaben ranar Asabar 18 ga watan Maris, da yin addu’ar Allah SWT ya shige masa gaba a duk tsawon mulkinsa.
Sannan kuma yayi kira ga gwamnati mai zuwa da ta tabbatar da kafa hukumar Hisbah kamar yadda gwamnati mai barin gado ta Aminu Bello Masari ta yi.
Daga karshe shugaban ya taya dukkan Musulmai murnar shigowar watan Ramadan na shekara 1444 AH da fatan Allah SWT ya karbi dukkan ayyuka, da dacewa da alkairan da ke cikin wannan wata.