Daga Bello Hamza,
Shugaban karamar hukumar Bwari, Mr John Gabaya, ya bukaci ma’aikatan karamar da ma al’ummar yankin baki daya su dukkan matakan kariya daga kamuwa daga cutar korona kamar yadda gwamnatin tarayya ta bayyana, shugaban karamar hukumar ya yi wannan bayanin ne a tattaunawarsa da ma’aikatan karamar hukumar a garin Bwari ranar Juma’a.
Shugaban ya kuma ce, bayanin akan haka ya zama dole ne musamman ganin yadda cutar ke cigaba da barna a sassan kasar nan, kuma mataki daya ne maganin sa na kaucewa kamuwa da cutar a harkokin mu na yau da kullum.
Ya kuma bukaci jami’an tsaro da ke aiki a ma’aikatar su tabbatar da duk wanda zai shiga ma’aikatar yana sanye da takunkumin kariya daga cutar kamar yadda aka tsara.
Bayanin ya nuna cewa, karamar hukumar ta kulle ayyukan ma’aikata na kwanaki goma kafin ta bude a ranar Alhami 21 ga watan Janairu 2021.
An refu ma’aikatan ne don a samu damar yin feshi da kuma zuba sinadari don kashe kwayoyin cuttuka a ma’aikatan, hakan kuma yana faruwa ne don ganin yadda cutar take karuwa a cikin yankin Abuja dama Nijeriya gaba daya.