An roki masu hannu da shuni da kuma ‘yan kungiyar tsoffin dalibai da su bada gudunmuwarsu domin tabbatar da samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa a kwalejin ilimi ta Isa Kaita dake Dutsinma.
Shugaban kwalejin Dr. Maigari Bello Abdu ya bayyana haka ga ‘yan kungiyar kwamitin tuntuba na garin Dutsinma karkashin jagoraincin Bello.
Kamar yadda yace karancin ajujuwa. Ababen zama, dakunan gwaje-gwaje, masallaci da kuma dakin kwanan dalibai na maza na daga cikin manyan abubuwan dake cima kwalejin tuwo a kwarya.
Dr. Maigari Abdu yayi kira ga masu hannu da shuni dasu gina gidaje daf da kwalejin domin badawa haya ga dalibai a cikin saukakakken farashi amatsayin gudummuwarsu ga bunkasa ilimi.
Haka kuma ya jaddada bukatar dake akwai ga ‘yan kungiyar tsaffin daliban kwalejin a kodayaushe su rika ziyartar makaranta domin tanatnce na’u’rorin kayayyakin koyo da koyarwar da zasu samar a matsayin tallafi.
Dr. Maigari Abdu yace kwalejin tana da dalibai sama da 8,000 don haka akwai bukatar kara fadada masallacin da take dashi domin masallata su kara samun wuraren gudanar da ibada.
Shugaban Kwalejin ilimi ta Isa Kaita ya koka matuka akan karancin ruwa da ake samu a gidajen haya na dalibai maza inda yayi kira ga mutane a garin Dutsinma dasu taimaka ma daliban.
Dr. Maigari Abdu ya tunatar da al’ummar garin Dutsinma dasu yi koyi da sauran jihohi ta fuskar bunkasa cigaban ilimi kasancewar gwamnati ita kadai ba zata iya warware dukkanin bukatun al’umma ba.
Tun da farko, shugaban kungiyar tuntuba na Dutsinma Bello Isiyaku ya yima shugaban kwalejin dan takaitaccen bayani akan aikace-aikacen kungiyar da kuma bukatar hadin gwiwa domin cigaban yankin.