Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA), ta rufe Olajumoke Akinjide Plaza, Dutse-Alhaji da ke Abuja, har sai baba-ta-gani bisa zargin matsaloli a kasuwar.
Ihkaro Attah, babban mataimaki na musamman ga ministan babban birnin tarayya a kan sanya idanu a ayyuka da tabbatar da bin doka, wanda ya jagoranci aikin, ya koka da yadda ake samun matsaloli na kara-zube da suka hada da zubar da shara a ko ina a kasuwar.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Hakimi Da Wasu Mutane 6 A Zamfara
- Wasu Da Ake Zargin ‘Yan Daba Ne Sun Kai Wa Magoya Bayan Atiku Hari A Jihar Ribas
“Mun ba da umarnin rufe Olajumoke Akinjide Plaza Dutsen-Alhaji har sai baba-ta-gani saboda rashin bin doka da oda da muka lura makonni biyu da suka gabata.
“Ana zubar da shara a ko ina a kasuwar kuma abun takaici ne, ga ‘yan karere a ko wanne lungu da sako, ba a kwashe dattin magudanun ruwa kuma an ma maida su wajen zuba shara.
“Dole ne mu rufe kasuwar kamar yadda Ministan Babban Birnin Tarayya, Malam Muhammad Bello ya umarta, har sai lokacin da za a magance kalubalen muhalli a kasuwar, hada-hadar haram da kuma kwashe shara.
“Kuma idan nan gaba muka zo nan kuma mun tabbata sun yi abin da ake bukata to za mu sake bude kasuwar.
“Amma sun tabbatar mana da cewa suna son fara aikin a yanzu kuma za a yi su cikin gaggawa kuma za mu zo mu duba domin a sake budewa amma a yanzu an rufe kasuwar ” in ji shi.