Yusuf Shuaibu" />

An Sace Jami’in INEC Da ‘Yan Bautan Kasa A Anambra

Gaidam

A halin yanzu dai, an bayyana cewa an sace jami’in hukumar zabe tare da masu yi wa kasa hidima a mazabar Indiokolo da ke karamar hukumar Orumba cikin Jihar Anambra ranar Asabar, lokacin da ke gudanar da zabe a Jihar. Duk da cewa an bayyana cewa an yi zabe cikin kwanciyar hankali a Jihar, an samu rikici zabe dan kadan a Jihar.
Kwamishinan ‘yan sandar Jihar Anambra Rabiu Ladodo, shi ya bayyana hakan lokacin da yake ba da ba’asi a kan zaben, ya bayyana cewa an sace wasu mutane lokacin da ake gudanar da zaben. Ya ce, “Zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali a dukkan yankunan da muka zaga a Jihar.
“Duk da an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali dai, an samu kananan rikici kamar na satar akwati a mazabar Onuma Imeobi da ke Onitsha. Sayan kuri’u, wargaza zabe a wasu mazabu da sace jami’in hukamar zabe da ‘yan bautar kasa a mazabar Indiokolo cikin karamar hukumar Orum ta Arewa da kuma karamar hukumar Anambra ta Kudu.”

Exit mobile version