Hukumar gidan gyaran hali ta Nijeriya ta ce ta sake kama wasu fursononi cikin wadanda suka tsere daga gidan yari a Maiduguri na Jihar Borno lokacin ambaliyar ruwan da aka yi a watan Satumba da ya gabata.
Kakakin hukumar, Abubakar Umar ya shaida wa BBC cewa an samu nasarar sake kama 51 daga cikin mutanen 271 da suka tsere.
- Yadda Gwamna Nasir Idris Ya Daura Damarar Bunkasa Ilimi A Jihar Kebbi
- Yadda Gwamna Nasir Idris Ya Daura Damarar Bunkasa Ilimi A Jihar Kebbi
Ya kuma ce suna aiki hadin gwiwa tsakaninsu da jami’an tsaro da dama, inda ya ce suna bai wa juna bayanan sirri da zai taimaka musu wajen yin aiki.
“Lokacin da abin ya faru, fursunoni 271 ne suka tsere. Yanzu mun yi nasarar sake kama 51 daga cikinsu,” in ji Umar.
Ya ce suna ci gaba da kokari wajen ganin sun kama wadanda suka rage.