Makonni uku da kashe wasu ɗaliban makarantar Adekunle Ajasin ta Jihar Ondo, Akungba-Akoko, wata dalibar makarantar saurayinta ya sake kashe ta.
Kisan na baya-bayan nan da aka yi wa Joy Adeyemi ta Sashen Nazarin Kiwon Lafiyar Jama’a na Cibiyar, ya haifar da zanga-zangar dalibai a Akungba, al’ummar jami’ar.
Idan dai za a iya tunawa, an yi garkuwa da wasu dalibai biyu da suka kammala karatunsu na makarantar, Andrel Okah na Sashen Tarihi da Nazarin ɗuniya da John Abba na Sashen Tattalin Arziki.
- Binciken Jami’ar Bayero Ya Gano A Hoton Yatsa Za A Iya Gane Mai Cutar Daji – Farfesa Darma
- Akwai Bukatar Daina Cin Zarafin Malaman Makaranta
daga baya jami’an ƴansanda sun kama wadanda ake zargin sun yi kisan, amma A wani labarin na baya-bayan nan, wata majiya ta shaida wa ɓanguard cewa saurayin nata ne ya kashe dalibar a ranar Talata, inda ya gudu daga cikin jama’a.
A cewar majiyar, “Wanda ake zargi da kisan an ce dan garin ne.
“Saurayin nata ne ya kashe marigayiyar a ranar Talata kuma ya kulle ta a cikin dakinsa, maƙwabta ne suka ja hankalin daliban a lokacin da suka fahimci wani wari daga dakin.
“Har yanzu ba mu san dalilin da ya sa saurayin ya kashe ta ba, dalibar tana sana’ar POS a yankin, amma tun ranar Talata, ta ɓace kuma babu wanda ya san inda take sai jiya, lokacin da maƙwabta suka ji wani wari daga dakin saurayinta.
“Shi yaron, bayan sun kashe ta, ya tafi da cinikin da yi a wajen sana’ar ta ta POS.
“Lokaci ya yi da gwamnatin jihar za ta yi wani abu game da kashe-kashen da ƴan asalin garin suke yi wa dalibanmu, idan ba a yi wani abu ba, hakan na iya haifar da mummunan rikici a wannan al’umma.
“Idan za ku iya tunawa a makonnin da suka gabata, an kuma sace dalibanmu biyu tare da kashe su, don haka dole a yi wani abu.”
A halin da ake ciki, daliban, a yayin zanga-zangar, sun rera waƙoƙin haɗin kai daban-daban, dauke da kwalaye da rubuce-rubuce irin su, ‘A Akungba Akoko, ka ce kada a kashe dalibai’, ‘A daina kashe mu, daliban AAUA,’ ƴa kamata gwamnatin jihar ta sa baki wajen kashe daliban AAUA,’ da dai sauransu.
da take mayar da martani game da sabon kashe-kashen da aka yi a cikin al’ummar jami’ar, kwamitin haɗin gwiwa na ƙungiyar daliban Nijeriya ta ƙasa, ta yi Allah-wadai da wannan danyen aikin tare da yin kira ga jami’an tsaro da su gurfanar da wanda ya aikata laifin.
“ƙungiyar daliban Nijeriya ta ƙasa, Joint Campus Council, Ondo Aɗis ta yi matuƙar kaɗuwa tare da nuna alhinin ta dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi wa daliban Jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba Akoko, Jihar Ondo.
Tuntubi kakakin rundunar ƴansandan jihar, Ayanlade Olayinka, ya tabbatar da kisan.
Ayanlade ya ce saurayin marigayin ya gudu daga cikin al’umma kuma nan ba da jimawa ba jami’an ƴansanda za su kamo shi.
Ya ce an kama mutane uku da ake zargin ana yi musu tambayoyi kan kisan da aka yi a jami’ar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp