Kasar Burkina Faso dai ta sake fuskantar wani juyin mulki, wanda shi ne na biyu cikin watanni takwas a kasar da ke yammacin Afirka.
Kyaftin Ibrahim Traore ne, ya sanar a daren Juma’a cewa sojoji sun kwace mulki tare da hambarar da shugaban sojoji Paul Henri Damiba.
- APC Ta Kafa Kwamitin Yakin Neman Zabe Na Mata, Ta Bayyana Aisha Buhari A Matsayin Jagora
- Manchester United Ta Tafka Asara
Shi kansa Damiba da wasu ‘yan ta’adda sun kwace mulki a watan Janairu daga hannun shugaba Roch Kabore.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Traore ya shaida wa mutanen cewa sojoji sun taimaka wa Damiba ya yanke shawarar cewa ba zai iya tabbatar da kasar ba.
Burkina Faso dai na kokawa da karuwar tashe-tashen hankula da suka yi sanadin mutuwar mutane tare da yin gudun hijirar wasu da yawa a yankunan da lamarin ya fi kamari.
“Sakamakon tabarbarewar lamarin, mun yi kokari sau da dama don ganin Damiba ya mayar da hankali kan batun tsaro,” in ji sabon shugaban.
Traore ya sanar da rusa majalisar dokokin kasar tare da rufe iyakokin kasar.
Haka kuma, an sanya dokar hana fita daga karfe 9 na dare zuwa 5 na safiya.
Damiba dai ya dawo ne daga taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 da aka gudanar a birnin New York na kasar Amurka.