A ranar Asabar ne jam’iyyar APC, ta sanar da jerin sunayen tawagar yakin neman zabenta ta mata.
Tawagar wadda aka kirkireta saboda yakin neman zaben Tinubu da Shettima, ana sa ran Uwargidan Buhari, za ta jagoranci bangaren mata na jam’iyyar zuwa ga nasara a matsayin babbar uwa ga jam’iyyar.
Daga cikin jagororin tawagar akwai Sanatan Legas ta Tsakiya, da kuma mai dakin tsohon gwamnan Jihar Borno, kuma abokin takarar Tinubu, Kashim Shettima.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Rinsola Abiola, diya ga marigayi Cif MKO Abiola, ta fitar a ranar Asabar.
Asabe Vilita Bashir, tsohuwar ‘yar majalisar tarayya daga Borno, za ta jagorancin tawagar yayin da Lauretta Onochie za ta mata mataimakiya.
A Arewa Maso Yamma kuwa, Dakta Zainab Bagudu, mata ga gwamnan Jihar Kebbi da Falmata Zulum mata ga gwamnan Jihar Borno ne za su jagorancin yankin.
Tawagar kwamitin ta kunshi manyan ‘yan siyasa na APC, da suka hada da tsofaffin hannaye da kuma ‘ya’ya da makusantan jam’iyyar ta APC.
Cikakken jerin sunayen wadanda aka yi wa mukami a kwamitin yakin neman zaben na mata yana shafin intanet na jam’iyyar.