Shugaban hukumar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci ta Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ya samu ‘yanci bayan shafe wasu awanni a hannun ‘yansanda. An sako shi daga shalƙwatar ‘yansanda ta Zone One a Kano cikin dare ranar Juma’a, bayan samun belin girmamawa.
Muhuyi ya yi bayanin halinsa da ake ciki ne ga wata tawagar sa ido daga ofishin Sufeto Janar na ’Yansanda, wadda ta kama shi bisa ƙorafin Bala Inuwa Mohammed, tsohon Manajan Daraktan KASCO, kan zargin almundahana ta Naira biliyan huɗu da kuma kadarorin da aka kulle da kuɗinsu ya kai biliyan biyu.
Lauyan Muhuyi, Usman Umar Fari, ya tabbatar da cewa an yi masa tambayoyi na tsawon sa’o’i uku tare da ba shi umarnin komawa Abuja don ci gaba da bincike ranar Litinin. Ya kuma yi tir da matakin ‘yansanda, yana cewa zargin na cikin kotu, amma an yi amfani da hanyoyin da ba su dace ba wajen ɗaukar mataki.