Wata kotun sauraren manyan laifuka a New York ta saki tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump bayan tsare shi na tsawon kwana daya.
An hangi Trump yana barin harabar kotun ta Manhattan, wanda aka zarge da biyan wasu mutane kudi ciki har da jarumar fina-finan badala kafin zaben 2016.
- Ramadan: Hisbah Ta Rufe Wuraren Shan Giya, Ta Hana Karuwanci A Jigawa
- Gwamnatin Kogi Ta Yi Allah Wadai Da Harin ‘Yan Bindiga Da Ya Kashe Mutane Da Dama A Jihar
A halin da ake ciki kuma, tsohon shugaban na Amurka a ranar Talata ya ki amsa laifinsa a kotun New York, yayin da ya zama shugaban Amurka na farko da aka kama bisa zarginsa da aikata laifuka, wanda tuni ya fara yakin neman sake zama shugaban kasar a shekarar 2024.
Trump dai ya ki amsa duk wasu tuhume-tuhume da ake zarginsa da aikatawa, wadanda rahotanni suka ce sun hada da laifin hada baki da kuma biyan wasu kudade domin togaciyar baki a yakin neman zaben 2016.