Rabiu Ali Indabawa" />

An Saki ’Yan Kasuwar Kantin Kwari Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Kantin Kwari

Kungiyar ‘yan kasuwar Arewa sun tabbatar da sakin ‘yan kasuwar da a ka sace. Kungiyar ta bayyana haka ne a wata hira ta wayar tarho ta bakin wani jigon kungiyar. Shugaban kungiyar ya tabbatar da cewa sai da a ka biya kudin fansa kafin sakin ‘yan kasuwar.

Kimanin ‘yan kasuwar Kantin Kwarin 18 ne aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Aba ta Jihar Abia, wadanda kuma a halin yanzu an an sake su da kyar. Idan za ku iya tunawa an sace ‘yan kasuwar ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Janairu, a Okene, Jihar Kogi, a kan hanyarsu ta zuwa Aba don sayan kayan masaku.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Arewa na Nijeriya, Alhaji Abubakar Babawo ya tabbatar da sakin ‘yan kasuwar a wata hira ta wayar tarho da jaridar The PUNCH a Kano ranar Lahadi.

Ya ce ‘yan kasuwar da a ka sace an sake su ne da yammacin ranar Asabar. “Yan kasuwar Kano 18 da ke cikin ‘yan kasuwar 27 sun kubuta a yammacin Asabar. Sun kwana a Kaduna, kuma yanzu haka suna kan hanyar zuwa Kano. “Muna tsammanin su yau a Kano kamar yadda muke tattaunawa da su. “Mun tattauna da wasu daga cikinsu. Dukkansu an sake su. Suna nan lafiya kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Kano.” In ji shi. Babawo ya tabbatar da cewa an biya kudin fansa amma kuma bai bayyana adadin kudin da aka biya don sakin su ba.

Exit mobile version