Ma’aikatar kula da ma’aikata da tabbatar da walwalar al’umma ta kasar Sin ta bayyana a jiya Alhamis cewa, daga watan Janairu zuwa Satumbar bana, an kara samar da guraban ayyukan yi ga karin wasu mutane miliyan 10.01 a kasar.
Duk da cewa ana fuskantar wasu matsaloli, amma ana samar da guraban ayyukan yi yadda ya kamata a kasar Sin, kuma daya daga cikin muhimman dalilan haka shi ne, manufofin da ake aiwatarwa a fannin taimakawa kamfanoni daidaita matsalolinsu. Alkaluman ma’aikatar kula da ma’aikata da tabbatar da walwalar al’umma ta kasar Sin sun nuna cewa, zuwa karshen watan Satumba, yawan kudin da aka ragewa kamfanoni ya zarce kudin Sin Yuan biliyan 280.
Baya ga haka, an kara kyautata hidimomin samar da guraban ayyukan yi. Ya zuwa yanzu, ma’aikatar kula da ma’aikata da tabbatar da walwalar al’umma ta gudanar da tarurruka a zahiri ko ta intanet, inda aka samar da guraban ayyukan yi sama da miliyan 100, don karfafa gwiwar cibiyoyin samar da hidimomin guraban ayyukan yi, wajen aiki yadda ya kamata.
Sai kuma, ana kara kokarin tallafawa mutane marasa galihu don su samu ayyukan yi. A karshen watan Satumba kuma, adadin mutane marasa galihu da suka samu aikin yi ya kai miliyan 32.69.
Sa’an nan, ana ci gaba da samar da horo kan fasahohin aiki. Zuwa karshen watan Satumba, an samar da horon fasahohin sana’a ga mutane sama da miliyan 16. (Murtala Zhang)