Connect with us

MANYAN LABARAI

An Samu Karin Mutum 238 Masu Koronavirus A Nijeriya, 92 A Kano

Published

on

Hukumar NCDC ta sanar da samun karin mutum 238 wadanda suka kamu da cutar Koronabairos a fadin Nijeriya. Kamar yadda aka saba duk dare hukumar tana sake adadin wadanda suka kamu a wannan ranar ta shafukkan sada zumuntar ta.

A wata daban kuma, jihar Kano kadai an samu adadin mutum 92 da cutar ta yi wa kamun kazar kuku, kamar wasa kullum adadin wadanda suka kamu a jihar ya na ta kara hauhawa.

Zuwa yanzu adadin masu cutar ya haura zuwa mutum 2,170, inda mutum 351 suka samu sauki, sai mutum 68 da cutar ta kashe.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: