Tsohon Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Nijeriya (1 Mechanised Division), Kaduna, Manjo Janar Danjuma Ali-Keffi (mai ritaya), ya bayyana cewa an gano wasu manyan mutane da ke da alaƙa da kuɗaɗen ta’addanci da safarar ɗanyen mai a Nijeriya, amma daga bisani aka ba su kariya ba tare da gurfana a kotu.
A wata hira da ya yi da tashar Arise News ranar Alhamis, Ali-Keffi, wanda ya taɓa jagorantar Operation Service Wing (OSW) da aka kafa domin toshe hanyoyin kuɗaɗen ƙarfafar ta’addanci, ya ce bincike ya gano masu ɗaukar nauyin Boko Haram, ciki har da waɗanda ke da alaƙa da manyan ƴan siyasa.
- Da Ɗumi-Ɗumi: Jami’an Tsaro Sun Kama Manyan Shugabannin Ƙungiyar Ansaru 2
- Rasha Ta Bayar Da Gawarwakin Sojojin Ukraine 1,000
Ya ce cafke shugabanni da masu ɗaukar nauyin Boko Haram a shekarun 2017–2018 ya raunana ƙungiyar matuƙa, abin da ya haifar da miƙa wuyan da yawa daga wajen mayaƙan Boko Haram tare da iyalansu, har ma da mutuwar shugaban ƙungiyar, Abubakar Shekau. Ya kuma bayyana cewa binciken ya samu tallafin bayanan leƙen asiri daga ƙasashen waje, ciki har da UAE, Birtaniya, da Amurka.
Sai dai tsohon Janar ɗin ya ce duk da gano alaƙar da ta shafi ƴan kasuwa, masu sufurin jiragen sama, da wasu ministoci da tsoffin manyan jami’an tsaro, daga bisani an saki wasu daga cikin mutanen da aka kama ba tare da shari’a ba. Ya ƙara da cewa ya kai ƙorafi ga Shugaban ƙasa a lokacin, amma daga baya aka nuna jinkiri har aka bari waɗannan manyan mutane suka tsere ba tare da hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp