Wasu mutanen da lamarin ya faru a kan Idonsu sun bayyana cewa, wasu fusatattun mutane sun kona wasu gine-ginen da ke cikin fadar Aree, a karamar hukumar Boripe ta Arewa da ke Jihar Osun.
An shiga firgici da rashin kwanciyar hankali yayin da maharan suka mamaye garin Iree a Jihar Osun.
Maharan sun cinnawa Fadar Aree ta Iree wuta a yammacin Alhamis.
Wasu shaidun kuma sun bayyana cewa ’yan bindiga ne suka kona gine-ginen.
Sun bayyana cewa wutar ta tashi sakamakon adawa da tsare Cif Soliu Atoyebi, Aogun na Iree da jami’an tsaron farin kaya (DSS) suka yi.
Lamarin dai kamar yadda rahotanni suka bayyana, ya sanya toshe mafi yawan hanyoyin da ke cikin garin.
Idan zaku iya tuna wa cikin watan Nuwamba wasu mutane da ke adawa da gwamnati suka kona fadar Akinrun na Ikinrun saboda nada Oba Yinusa Olalekan Akadiri.
An kona fadar Akinrun ne domin a hana sarki shiga.
Ana cikin haka kuma aka harbe Lukman Omoola, wani dan asalin garin.