Runduna ta 3 ta sojojin Nijeriya da ke Rukuba, kusa da Jos, ta shirya addu’o’i ta musamman a ranar Juma’a don bikin cika shekara 159 da kafa runduar sojojin Nijeriya.
Jim kadan bayan gudanar da addu’o’in, Babban Kwamamndan Barikin, Manjo Janar Ibrahim Ali, ya ce an shirya taron ne don neman kariyar Allah a kan matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar nan gaba daya.
- Sojoji Sun Ceto Wata ‘Yar Makarantar Chibok Da Boko Haram Suka Sace, Ruth Bitrus, A Borno
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 3 Da Kwato Makamai A Wani Farmaki Da Suka Kai Musu
”A daidai ranar 6 ga wata Yuli rundunar sojojin Nijeriya za ta cika shekara 159 da kafuwa, akan haka zamu yi wanann gaggarumin bikin, saboda haka aka ware mako daya cur don gudanar da wannan bikin.
”A yau mun gudanar da addo’in ne don neman karin zaman lafiya da samun nasara a kan matsalolin tsaron da ake fuskanta a sassan kasar nan,” in ji shi.
Ya kuma kara da cewa, shugaban rundunar Sojojin Nijeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya, yana garin Owerri don gudanar da irin wannan bikin.
Tun da farko, Babban Limamin Barikin, Kanal Abubakar Tahir, ya bukaci al’umma Musulmi su bayar da goyon bayan su don tabbatar da hadaddiyyar kasa mai cike zaman lafiya..
Ya ce, addinin Musulunci ya yi tir da duk ayyukan ta’addanci da duk wasu nau’in ayyukan tayar da hankali a cikin al’umma.