Kamfanin Dangote (DIL) ya zargi Kamfanonin Mai na ƙasa da ƙasa (IOCs) da ke aiki a Najeriya da laifin kawo cikas ga ayyukan matatar man Dangote da gangan ta hanyar ƙara farashin ɗanyen man da ake samu a cikin gida.
Mataimakin shugaban kamfanin mai da iskar gas na DIL, Devakumar Edwin, ya bayyana hakan ne a wani taron horas da ‘yan jarida masu samar da makamashi, inda ya zargi hukumar IOC da neman kuɗaɗen da ya wuce kima ko kuma cewa babu ɗanyen mai, wanda hakan ya tilastawa matatar Dangote biyan ƙarin Dala 6 sama da farashin kasuwa a lokaci guda.
- Hauhawar Farashin Siminti: Majalisa Ta Bai Wa Dangote, BUA, Da Sauransu Wa’adin Kwanaki 14 Su Bayyana Gabanta
- Fara Aikin Matatar Dangote Da Ta Fatakwal: Jama’a Na Dokin Karyewar Farashin Fetur
Duk da ƙoƙarin da Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ke yi na ganin an cika wajibcin samar da ɗanyen mai a cikin gida (DCSO), Edwin ya ba da shawarar cewa IOCs na lalata wannan yunƙurin.
Ya kuma jaddada cewa, NUPRC ta himmatu wajen cimma wannan ƙuduri, inda ya yi tsokaci kan taron da suka yi a baya-bayan nan da masu samar da ɗanyen mai da masu matatun man don aiwatar da dokar da ta kafa dokar masana’antar mai (PIA).
Edwin ya zargi IOCs da yunƙurin yin zagon ƙasa ga nasarar da matatar ta samu, wanda hakan ya tilastawa matatar da Dangote ya nemo ɗanyen mai daga wurare masu nisa da tsada kamar Amurka.
Wannan lamarin yana ƙara ta’azzara tsadar kayan aikin matatar tare da kawo cikas ga aikinta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp