Rundunar ‘yansanda Nijeriya a Abuja ta tsaurara matakan tsaro da tura karin jami’anta sassa daban-daban a babban birnin tarayya domin tabbatar da tsaro yayin da ake shirye-shiryen bukukuwan karshen shekara.
Rundunar ta ce ta tura dakaru na musamman duk yankunan da ke bukatar sa ido domin dakile duk wani yunkurin tada zaune tsaye ko bata gari, kamar yada kakakin ‘yansanda Abuja, Josephine Adeh ta tabbatar a wata sanarwa.
- Kanu Ya Yi Tur Da Kai Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Kudu Maso Gabas
- 2023: INEC Ta Gargadi Masu Sayar Da Katin Zabensu Ga ‘Yan Siyasa
Sannan an garagadi jami’an da su gudanar da aikinsu cikin kwarewa da kaucewa duk wasu halaye da zai bata sunansu ko zubar da mutuncinsu a idon al’umma.
Sannan su fitar da wasu lambobin kar-ta-kwana da mutane ke iya kira idan sun tsinci kansu cikin wani yanayi.
A baya-bayan nan Abuja ta shiga rudani biyo bayan wani rahota da ofishin jakadancin Amurka da Birtaniya suka fitar kan yiwuwar kai hare-haren ‘yan bindiga a birnin.
Sai dai tun a wancan lokaci hukumomin tsaro suka lashi takobin yaki da duk wata barazana da za ta shafi birnin.