Rabiu Ali Indabawa" />

An Tsaurara Matakan Tsaro A Kaduna Yayin Da Zanga-zanga Ke Yaduwa

Matakan Tsaro

An jibge matakan tsaro a garin Kaduna da gidan gwamnatin jihar. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da zanga-zanga ke bazuwa a fadin kasar, Ko a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, sai da masu zanga-zangar suka bukaci ganin Gwamna Nasir El-Rufai a gidan gwamnati. An tsaurara matakan tsaro a kewayen birnin Kaduna da gidan gwamnati a ranar Talata, 20 ga Oktoba yayin da zanga-zangar #SecureNorth ke kara yaduwa a fadin kasar, Majiyarmu ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa an gano motocin ‘yan sanda jibge a kewaye da shataletalen gidan gwamnati tare da ‘yan sanda masu kayan aiki da misalin karfe 10:00 na safe.
Masu zanga-zangar sun je gidan gwamnati a ranar Litinin inda suka ce lallai sai sun ga Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai. A ranar Talata masu zanga-zanngar sun taru a majalisar dokokin jihar da misalin karfe 12:00 na rana tare da ganga da kayen kida suna rawa da ihun “A tsare Arewa Yanzu”, “A kawo karshen ta’addanci,” da kuma fadin “A kawo karshen garkuwa da mutane.”

Exit mobile version