Connect with us

LABARAI

An Yaba Wa el-Rufa’i Kan Nadi Shugaban ‘’OPERATION ‘’Yaki

Published

on

An bayyana nadin tsohon mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya Alhaji M. M.Abbas a matsayin shugaban hukumar tsaro ta ‘O’PERATION Yaki’’ a jihar Kaduna da cewar babban hangen nesa ne da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed el’Rufa’i ya yi na nada wannan bawan Allah da tsawon rayuwarsa ya yi ne a batun tsaro a sassan Nijeriya, da kuma wasu kasashen duniya. Wani shugaban al’umma da ke Zariya, mai suna Alhaji Uba Zariya, wato Alhaji Uba Lamuni, ya bayyana haka a zantawarsa da wakilinmu da ke Zariya, kan wannan nadi da gawamna Malam el-Rufa’I ya yi a kwanakin baya.

Alhaji Uba Lamuni ya ci gaba da cewar, babu ko shakka, in har aka ba Alhaji M.M. Abbas  damar da ya kamata, matsalolin tsaro da ke addabar jihar Kaduna, zai iya zama tarihi a dan lokaci kadan.

Mai taimaka wa al’ummar ya kara da cewar, in an dubi yadda kafin a nada Alhaji M.M.Abbas a matsayin wannan mukami, an sami matsaloli a kan  tsaro, musamman a yankunan da suka hada da Birnin Gwari da kuma wasu sassan jihar Kaduna.Wannan matsala, kamar yadda Alhaji Uba Lamuni ya ce,ya yi amannar Alhaji M.M.Abbas zai fuskanci wannan matsala kuma ya warware matsala a cikin gaggawa. Sai dai kuma Alhaji Uba Lmuni ya yi kira ga daukacin bangarorin tsaro da suke jihar Kaduna, da su ba sabon shugaban rundunar tsaron na jihar Kaduna duk goyon bayan da suka kamata, domin ya sami damar samun saukin fuskantar ayyukan da aka dora ma sa. Dangane da wannan  goyon baya  Alhaji Uba Lamuni ya ce ya dace Alhaji M.M.Abbas ya samu, shi ne zai sami damar kawo karshen matsalolin kamfar tsaro da za a iya cewar, ba domin gwamna Malam Nasir na da kishin al’umma ba, da matsalolin tuni sun zama gagara badau a sassan jihar Kaduna baki daya.

Kan haka, ya kuma yaba wa daukacin ‘yan majalisar Kaduna na yadda suka ba gwamnan jihar Kaduna shawara da kuma goyon baya, na lokacin da ya yunkura zai nada Alhaji M.M.Abbas shugaban rundunar ‘’OPERATION ‘’Yaki a jihar Kaduna,ya ce. Ya dace al’ummar jihar Kaduna su ci gaba da yaba ma su, na hannun da suke da shi na nadin wannan bawan Allah.

A karshen ganawarsa da wakilinmu  Alhaji Uba Lamuni, ya yi kira ga

daukacin wadanda mai girma gwamnan jihar Kaduna ya nada su mukamai da su tashi tsaye na ganin sun rike amanar da gwamna ya dora su a kai tare da tallafa wa al’umma,na matsalolin da suke addabarsu.

Advertisement

labarai