• English
  • Business News
Saturday, October 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yanke Wa Da Nijeriya Hukuncin Daurin Shekara 4 Saboda Damfara A Amurka

by Sadiq
3 years ago
Nijeriya

Wata kotu a Kasar Amurka ta yanke wa wani dan Nijeriya mai suna Solomon Ekunke Okpe, dan shekaru 31, hukuncin daurin shekaru hudu da wata daya a gidan yari, bisa samunsa da hannu a wata kungiyar masu aikata laifuka ta Intanet.

Kungiyar ta masu aikata laifuka da ke aiki a kasashen Najeriya da Malesiya, da dai sauran wurare, wadanda suka aiwatar da zamba ta hanyar amfani da yanar gizo.

  • Atiku Ba Zai Yi Ritaya Daga Siyasa Ba -Dino Melaye
  • Kasashen Sin Da Honduras Sun Kulla Huldar Diflomasiyya

A cewar takardun kotu, tsakanin watan Disamba na 2011 zuwa Janairun 2017, Solomon Ekunke Okpe tare da abokansa da suka aikata laifin, sun kirkiri wata hanyar damfara ta amfani da hanyar imel na kasuwanci (BEC), na aiki-daga gida, da fidda kudi ta amfin da check din banki, soyayya, katin banki don damfarar mutane da ba su ji ba basu gani ba, bankuna, da masana’antu a Amurka da sauran wurare, wanda yin hakan zai haddasa asarar fiye da dala miliyan daya ga Amurkawa da wadanda lamarin ya shafa. Cikin wadanda lamarin ya rutsa da su har da kamfanin First American Holding, da bankin MidFirst.

Okpe da abokansa sun kaddamar da hare-haren satar bayanan sirri na imel don satar muhimman bayanan mutane, da yin kutse ta yanar gizo, don aiwatar da damfarar, suka rika yin amfani da bayanan suna damfarar mutane, bankuna, masana’antu, sun kuma yi safarrar, da amfani da katunan banki da aka sace don ci gaban damfararsu.

Okpe da hadakarsa sun kuma gudanar da zamba ta hanyar soyayya ta shafukan soyayya na yanar gizo, da nuna sha’awar mu’amalar soyayya da mutane da sunayen karya, don mutane su tura musu kudade zuwa ketare ko zamba ta hanyar waya. Okpe ya sa dubban mutanen sun fuskanci asarar dubban daloli ta hanyar soyayya.

LABARAI MASU NASABA

Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba

A baya dai an kama Okpe a Malaysia bisa bukatar Amurka kuma an tsare shi sama da shekaru biyu a lokacin bayan da ya nemi a mika shi ga Amurka.

A ranar 20 ga Maris, aka yanke wa daya daga cikin wadanda suka hada baki da Okpe, Johnson Uke Obogo, hukuncin daurin shekara daya da kwana daya a gidan yari, dangane da rawar da ya taka wajen zambar kudade.

FBI ta gano adadin wadanda abin ya shafa, duk da haka, akwai wadanda har yanzu ba a tantance su ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Manyan Labarai

Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

October 11, 2025
Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba
Tsaro

Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba

October 11, 2025
Babban Kwamanda Ya Jagoranci Ceton Mutanen Da Aka Sace A Kwara
Tsaro

Babban Kwamanda Ya Jagoranci Ceton Mutanen Da Aka Sace A Kwara

October 11, 2025
Next Post
Ahmed Musa Ya Kamo Tarihin Da Zidane Ya Kafa A Kwallon Kafa

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wata Ba’amurkiya Da Ta Ziyarci Saurayinta A Jihar Delta

October 11, 2025
Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

October 11, 2025
Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano

Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano

October 11, 2025
Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

October 11, 2025
Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

October 11, 2025
sallah

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida

October 11, 2025
Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.