Wata babbar kotu a garin Fatakwal na Jihar Ribas, ta yanke hukuncin kisa kan wani tsohon dan sanda da aka samu da laifin kashe wani direban motar bas saboda cin hancin Naira 100 a 2015.
Mai shari’a Elsie Thompson lokacin da take yanke hukuncin, ta ce shaidun da aka gabatar a gaban kotu sun nuna cewa tsohon sajan din James Imhalu, ya yi harbin bindiga da gangan kan direbar motar hayan, David Legbara tare da kashe shi nan take.
- Za Mu Yi Maganin ‘Yan Siyasar Da Ke Bai Wa Matasa Kwaya — NDLEA
- Buhari Zai Tafi Portugal Yau Talata Don Halartar Taron Majalisar Dinkin Duniya
Mai shari’ar ta bayyana tsohon sajan din James Imhalu a matsayin makashin da bai kamata a bar shi ya ci gaba da rayuwa ba a cikin al’umma.
Ta ce kotun ta samu tsohon dan sandan da laifi saboda amsa tuhuma kan abin da aka aikata da shaidun da aka gabatar a kansa.
Lauyan da ke shigar da kara, Kingsley Briggs, ya yaba da hukunci, inda ya ce zai kwantar da hankalin iyalan mamacin kasancewar shi ne mai kula da iyayensa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp