Wata babbar kotu a Jihar Katsina ƙarƙashin Mai Shari’a I. I. Mashi, ta yanke hukuncin kisa ga wasu ma’aikata biyu kan samun su da laifin kashe tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Jihar Katsina, Rabe Nasir.
Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Shamsu Lawal, tsohon mai gadin gidan da mai dafa abinci, Tasiu Rabiu.
- 2027: Ba Mu Kafa Haɗakarmu Don Cika Burin Atiku Ba – ADC
- Faransa Za Ta Fara Jefa Kayan Agaji Ta Sama A Gaza
Rahotanni sun nuna cewar waɗanda aka yanke wa hukuncin sun kashe Rabe a ranar 8 ga watan Disamban 2021 a gidansa da ke rukunin gidaje na Fatima Estate a Katsina.
Kotun ta bayyana cewa mutanen biyu sun sa wa Rabe guba domin kashe masa ƙarfin jikinsa, don su samu damar yi masa sata.
Amma an kama su bayan an gano gaskiyar lamarin.
Binciken likitoci da ‘yansanda ya tabbatar cewa gubar ce ta yi sanadin mutuwarsa.
Haka kuma, kotun ta yanke wa wani mutum mai suna Sani Sa’adu hukuncin ɗaurin shekara biyar saboda ɓoye gaskiya da ya yi dangane da wata Gift Bako, wadda ake zargi da hannu a kisan.
Lauyoyin waɗanda aka yanke wa hukunci sun nemi sassauci saboda suna da iyalai, amma lauyan gwamnati ya bayyana jin daɗinsa da hukuncin, inda ya ce an yi adalci kamar yadda doka ta tanada.
Rabe Nasir, ya taɓa zama ɗan majalisar tarayya da kuma kwamishinan Jihar Katsina a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Aminu Bello Masari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp