Mahdi M Muhammad" />

An Yanke Wa Soja daurin Shekaru 55, Saboda Kashe Ma’aikacin Hukumar WHO

A ranar Larabar da ta gabata ne babban kotu karkashin jagorancin Manjo Janar P. Fekrogha ta yanke hukuncin daurin shekara 55 a gidan yari ga soja mai suna Lance Corporal Babangida Ibrahim saboda kisan wani ma’aikacin kungiyar Lafiya ta Duniya WHO, Bello Abdullahi a jihar Zamfara da sace dukiyar sa.

Babban kotun, wacce ta ke a Command Officers Mess 1, Asokoro, Abuja, ta samu Ibrahim da laifi a kan dukkan tuhuma hudun da ake masa. An yanke wa mai laifin hukuncin shekaru 40 a gidan yari, sannan kuma an ba shi karin shekaru biyar a kan wadancan shekarun, kuma dukkan Sharuddan zasu gudana a lokaci guda ne.

Kotun ta ji cewa, Ibrahim yayin da yake aiki a kan Operation Mesa don yakar ‘yan fashi a jihar Zamfara, da misalin karfe 10 na dare, a ranar 11 ga Agusta, 2014, ba tare da dalili ba ya harbi Abdullahi da bindigarsa mai kirar AK47. Ya kuma shiga gidan Abdullahi da ke garin Gidan-Dari, na karamar hukumar Anka , Jihar Zamfara, kuma ya saci wayar Gionee E3 da wayar salularsa ta Nokia.

Sojojan ya kuma sace motar Honda Accord mallakar mamacin dauke da kwamfutar laptop daya da N6,000, wanda ya tuka ta zuwa Kaduna inda danginsa suke zaune kuma suna amfani da shi kafin masu bincike su kama shi.

Shugaban hukumar GCM ya ba da sanarwar cewa, Sojojin Nijeriya ne suka sanar da tabbacin hukuncin. Mambobin kungiyar GCM din sun hada da Brigs. Gen. J. Ochai, P. Pearse, E. Ikomi, A. Okpodu, S. Makulo; Cols. M. Ibrahim, L. Abubakar, M. Yusuf da Alkalin Alkalai, Kaftin K. Ogili.

Exit mobile version