Babban rukunin gidan radiyo da talibiji na kasar Sin wato CMG tare da hadin kai da kamfanin yada labarai na kasar Brazil sun gabatar da bikin cudanyar al’adu na musamman, domin murnar cika shekaru 50 da kafuwar huldar difilomasiyya tsakanin Sin da Brazil, a daidai lokacin da Xi Jinping ke halartar taron kolin G20 karo na 19 da ziyarar aiki a kasar, a jiya Laraba, a Brasilia hedkwatar kasar.
Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi cewa, CMG na fatan hadin gwiwa da al’ummar Brazil don zurfafa cudanya da mu’ammalar al’ummun biyu, da ma gaggauta raya huldar abota bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu zuwa wani sabon mataki. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp