Daga Muh’d Shafi’u Saleh,
Wasu da’ake zargin masu garkuwa da mutanene, sunyi garkuwa da dan majalisar dokokin jihar Taraba Honarabul Bashir Muhammad Nape, dake wakiltar mazabar Nguroji, a gidansa dake Jalingo fadar jihar.
Rahotannin dake fitowa daga inda lamarin ya auku sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar da su ka saceshin sun taho da yawa, inda su ka rika harbe-harbe sun kori ‘yan bangar dake gadi a gidan dan majalisar.
“Yan bindigar sun taho da yawa, sun farma ‘yan banga da ke gadin gidan su ka kutsa cikin gidan kai tsaye zuwa har inda dan majalisar ke kwana..
“An ce ‘yan bindigar sun zo gidan ne da babura da misalin karfe 1:00 na daren yau Laraba, yayin da mutane ke barci.
“Da shigarsu gidan, su ka kwace duk wayoyin salularshi da na mutanen da ke gidan.
“Daganan ne su ka tafi da mamban sun hau babur dinsu sukl ka tisa keyarsa ba tare da sunce komai ba,” in ji wani da ke kusa da gidan dan majalisar.
Wannan dai shi ne karo na biyu da ‘yan bindiga ke sace dan majalisar dokokin jihar Taraba cikin shekarun guda. Haka kuma a 30 ga Disamban 2017, an sace dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Takum 1, a garin Takum lokacin da ya je domin gudanar da bukukuwan karshen shekara, inda su ka kasheshi bayan an biya kudin fansa.
Kokarin jin tabakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba kan wannan batun ya ci tura, domin kuwa Kakakin rundunar DSP David Misal, baya tafiya lokacin hada rahoton.