Abdullahi Sheme" />

An Yi Kira Ga Shugabanni Su Ji Tsoron Allah

An yi kira ga shuwagabanni da su ji tsoron Allah. Wannan kiran ya fito ne daga bakin Sheikh Nuraddeen Adamawa a lokacin da ya ke rufe tafsirin watan Ramadan na wannan shekara a babban masallacin Juma’a na  Unguwar Magajin Makera da ke Funtuwa a jihar Katsina, a ranar Juma’ar nan databagata 31/05/2019 da misalin karfe biyar da rabi na yamma 5:30.

Sheikh Nuraddeen wanda yasaba zuwa duk shekara domin gudanar da tamsiri a Masallacin yaci gaba dacewar kiran yazama wajibi ganin yadda al’amarin rayuwa yakasance, mafi yawan ‘yan kasa suna cikin tsadar rayuwa, yace babu shakka mutane suna cikin rashin kudi da rashin tsaro a wadansu sassan kasar nan.

Babban Malamin yace shuwagabanni su tuna gobe kiyama Allah madaukakin sarki zai tambayesu yadda suka gudanar da mulkinsu, yace su dai malamai iyakacinsu su tunasar da al umma abinda Allah yace.

Malamin yaci gaba da kira ga sauran al umma da suji tsoron Allah sutaimaki ‘yan uwansu mara shi kuma su fidda zakkar su yadda addinin Musulunci ya tanada, kuma aguji sabon Allah, kuma mutane su tashi tsaye wajen yin addi’o in zaman lafiya da karuwar arziki a kasa, musamman wadannan kwanaki da suka rage a cikin wannan wata mai albarka.

Kungiyar Izalatul bidi’a wa’ikamatus sunna ta kasa ce ta turoshi domin gudanar da wa’azin duk shekara.

Sheikh Nuraddeen ya taba zama mai baiwa gwamnan jihar Adamawa shawara akan aikin Hajji; sannan Malam yaci gaba da kira ga Gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen magance yawan satar al umma da akeyi domin neman kudin fansa. Jihar Katsina jihace ta manoma, yakamata Gwamnatin tarayya ta kawo masu dauki a sami zaman lafiya kuma a samar ma manoma ingantaccen taki kuma cikin lokaci, babu shakka Gwamnatin Jihar Katsina tana kokari sosai.

Daga karshe yana godiya ga al’umar garin Funtuwa akan yadda suka daukeshi da karamci kuma suna zuwa sauraren wa’azinshi, yace Funtuwa tazama garnish na biyu.

Exit mobile version