Daga Ibrahim Muhammad,
An yi kira ga yan kasuwa su rika sassautawa da yin hakuri da da karamar riba musamman a wannan lokaci da Azumin watan ramada ke karatowa.
Wani Matashin dan kasuwa a kasuwar Kantin Kwari Alhaji Sagir Haruna Daurawa ya yi kiran da yake zantawa da ‘yan jarida.
Ya ce, abin takaici ga wasu yan Kasuwar sai irin wannan wata mai albarka yazo wasu ke kokarin tsawwala kayan su yi tsada wanda hakan bai kamata ba.
Alhaji Sagir Haruna wanda shi ne shugaban Shagon “Haruna Daurawa Tedtile” yayi rokon dan Allah da Annabi kowane kaya na sayarwa ‘yan uwansa ‘yan kasuwa su sayar dashi a matsayinsa cikin adalci da kowa zai samu ya fita kunyar iyalinsa.
Sannan ya yi kira ga mata batagari da suke shigowa kasuwa da shiga ta kamala amma su rika sata bai kamata mata da ke da daraja da mutumci ace su ake samu da irin wannan ba don haka, masu irin wannan hali su yi hakuri su daina kar a kamasu ayi musu wulakancinda ta yiwu wani da ya sansu yaje ya fada hakan ya jawo zubewar mutuncinsu dana ya’yansu.
Ya ce kowace mace ta yi hakuri na tsayawa a matsayin da Allah ya ajiyeta domin zafin nema ba shi ne ke tara wani abu ba ayi hakuri a nemi taimakon Allah sai a sami abinda ake so na halak.
Da ya juya kan yanda ake samun matsalar sadarwa a kasuwar Kwari, ya ce, hakan na jawo musu tangarda da abokan huldarsu harma da iyalansu da basa samun ganawa da su ta waya in bukatar hakan ta taso. Sannan sukan rasa mu’amala da abokan huldarsu saboda sukan kirasu su kasa samunsu.
Ya ce sai dai yanzu an dan soma ganin saukin matsalar ta sadarwa, saboda mutane sun cire na’ura da suke sawa dake zuko damar kira.
Ya ce, yakamata kamfanonin waya suzo su duba su baiwa kasuwannin Kano network mai inganci dan kyautata huldarsu da suke a kasuwar da baya wuce na daga safe zuwa yamma aannan itama Gwamnati yakamata tasa baki wajen sanya kamfanonin sadarwa kyautata ingancin sadarwa a Kano.
Alhaji Sagir Daurawa ya ce suna hulda da yan kasashen waje daban-daban amma sakamakon barazanar tsaro huldar ta danyi rauni saboda basa iya zuwa mutum.bazai iya debo dukiyarsa yazo ko ya turo da ita ba, matsala ta auku ba wanda zai kama dan haka basa son zuwa.
Alhaji Sagir Haruna Daurawa yace koma da an turo da kudi ance ka tura kaya in an tura kayan suma direbobi da suke kaiwa na fadawa cikin barazanar rashin tsaro da sauran matsaloli wannan babaan kalubalene da ake fuskanta da suke rokon Allah ya kawo karshen abin ta baiwa kasarnan zaman lafiya da kwanciyar hankali.