Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya bayyana cewar, an yi ta tura masa sakonnin barazanar kisa kawai don aiwatar katin shaidar dan kasa (NIN) da rijistar tantance masu amfani da layukan waya a fadin kasar nan.
Pantami wadda ya shaida hakan a wajen taron shekara-shekarashekara-shekara na karo na hudu wanda ake yi duk ranar 16 g watan Satumban kuma hukumar kula da shaidar katin dan kasa (NIMC) ta gudanar a Abuja.
Ya ce sun maida hankali wajen amfani da fasahar sadarwar zamani wajen taskace bayanai tare da karfafa ‘yan kasa da su rungumi hakan amma wasu mutane kuma sai suka juya kansa wadda hakan bai musu yadda suke so ba.
“An yi ta barazana ga rayuwata saboda gabatar da tsarin NIN da rijistan layuka. Na yi imanin babu wani da zai iya sarrafa rayuwata a duk duniyar nan, Allah ne kadai. Mun dake kuma yanzu haka tsarin na aiki.
“Wasu lokutan na kan iya kwashe wata guda ma ba tare da na yi magana da NIMC ba kuma babu wata matsala. A yau, mafiya yawan wadanda muka yaka yanzu sun yi tsit. Idan aka koma shekaru uku aka yi waiwaye, hukumar kula da shaidar dan kasa (NIMC) na aiki ne cikin mawuyacin hali, don cimma alkaluman rijista ga kusan miliyan 90 ga kasar.
“A lokacin da na fara kula da NIMC adadin cibiyoyin rijista ba su wuce 1,000 ba, amma a yanzu, muna sa sama da 50,000. Tsarin taskace bayanai na tafiya yadda ya kamata. Mun kafa manufofin da tsare-tsaren kasa guda 19 kuma dukkaninsu an aiwatar. A tarihin Nijeriya ba a taba samun hakan ba,” Inji Ministan.
Ya bayyana cewar sashin ICT ya bada gudunmawa kaso 18.44% na kudaden shigar Nijeriya a 2022.
Darakta-janar na hukumar NIMC, Injiniya Aliyu Abdulaziz, ya ce suna hadin guiwa da sarakuna domin kara wayar da kan al’umman musamman na yankunan karkara da kan muhimmanci rijistan NIN.