Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙaddamar da shirin “Girl Effect Oya Campaign” domin yaƙi da cutar sankarar mahaifa da kuma rashin abinci mai gina jiki a tsakanin ‘yan mata, musamman masu shekaru 9 zuwa 14. Shirin wanda aka ƙaddamar a cibiyar Gusau Institute da ke Kaduna, ya samu nasarar rigakafin fiye da yara mata 754,304 da allurar HPV, wanda ke hana kamuwa da sankarar mahaifa.
Mataimakiyar Gwamnan jihar, Dakta Hadiza Balarabe, ta ce yaƙin yana da nufin ƙara wayar da kai tare da haɗin gwuiwar iyaye, malamai, shugabannin addini da na gargajiya don yakar jita-jita game da rigakafi da kuma ƙarfafa matakan rigakafi tun da wuri. Ta bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinar harkokin jin daɗin al’umma, Hajiya Rabi Salisu, inda ta ce: “Wannan kira ne na ɗaukar mataki, kira ne na tashi tsaye domin kare rayuwar ‘yan matanmu.”
- Ɗan Shekaru 15 Ya Kashe Wani Matashi Kan Rikicin Gona A Jigawa
- PSC Ta Amince Da Ɗaga Darajar Jami’an ‘Yan Sanda 12 Daga Matakin CP Zuwa AIG, Da Sauransu
Mataimakiyar ta ƙara da cewa, shirinsu na HPV wanda aka ƙaddamar a shekarar 2024 ya sanya jihar Kaduna cikin sahun gaba wajen kula da lafiyar matasa a Arewacin Najeriya. “Babu wani yaro ko yarinya da ya kamata a rasa saboda cutar da za a iya rigakafinta. Kowace yarinya a Kaduna tana da haƙƙin girma cikin lafiya da kwanciyar hankali,” in ji ta.
Ta yabawa ma’aikatan lafiya da suka tsaya a gaba wajen tabbatar da nasarar shirin, tare da kira ga masu ruwa da tsaki da su ci gaba da yaɗa wannan kira a cikin gidaje, da makarantu, da kasuwanni da masallatai ko coci, domin gina al’adar rigakafi da ɗaukar alhakin kare lafiya.
Kwamishinar ta jaddada cewa gwamnatin Malam Uba Sani za ta ci gaba da faɗaɗa samun rigakafi, ingantaccen abinci mai gina jiki da sauran ayyukan lafiyar matasa domin tabbatar da lafiyar ‘yan mata a jihar. Ana yabawa tsarin Kaduna a matsayin abin koyi wajen hada lafiyar matasa da rigakafi da kuma manufofin ci gaban al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp