Masarautar ’Yandoton Daji da ke jihar Zamfara, ta nada kasurgumin dan bindigar nan da ake nema ruwa a jallo, Ado Aleiro, sarautar Sarkin Fulanin ’Yandoto a ranar Asabar.
Aleiro dan bindiga ne da ya yi kaurin suna a ciki da wajen jihar Zamfara.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mai Juna Biyu A Kaduna
- Zaben Osun: ‘Yan Nijeriya Na Kallon Mu – Mahmoud Ga Ma’aikatan INEC
A baya gwamnatin Zamfara da wasu jihohi da ke makwabtaka da jihar sun yi kokarin yin sulhu da neman zaman lafiya daga hare-haren da shi da yaransa ke kai wa kauyukan jihar.
An gudanar da bikin nadin ne ’yan sa’o’i bayan masarautar ta sanar da fasa nadin tun da farko.
Sarkin na ’Yandoto, Alhaji Aliyu Marafa tun da farko ya yi shirn nada Aleiron sarautar a ranar Asabar, amma ya dage bikin ’yan sa’o’i sakamakon umarnin gwamnatin jihar, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Nadin na zuwa ne biyo bayan rawar da masarautar ta taka a baya tsakanin masarautar da ‘yan bindigar da suka addabi karamar hukumar tsafe a jihar.
Gwamnatin jihar dai tun da farko ta ba da umarnin dakatar da nadin ne saboda gudun cece-kucen da hakan zai iya jawowa idan labarin ya fita.
Bikin nadin sarautar dai, wanda aka yi a fadar masarautar ’Yandoton Daji, ya samu halartar Shugaban Karamar Hukumar Tsafe da kuma Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, DIG Mamman Tsafe (mai ritaya).
Wata majiya ta shaida cewar “Bikin ya kuma samu halartar shugabannin ’yan bindiga da dama tare da dakarunsu da suka je a kan babura.
“Sun bi ta hanyar Gusau zuwa Funtuwa, inda suka yada zango a Gidan Dawa, inda mutanen garin suka ba su katan-katan na lemukan sha a matsayin gudunmawa,” inji majiyar da ta bukaci a sakaya sunanta.
“Amma babu tabbaci ko shi Aleiron ya yi jawabi yayain nadin, amma daya daga cikin na hannun damansa wanda ya yi jawabi ya koka da yadda ya ce mutane na kiransu da ’yan ta’adda,” inji mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Sufyan.
“Mu ba ’yan fashi ba ne kuma ba ’yan ta’adda ba, amma muddin ana so zaman lafiya ya dawo, dole gwamnatin jiha da ta tarayya su samar mana mu makiyaya da filayen kiwo da makarantu da asibitoci.,”
A baya Aleiro ya yi alkawarin ajiye makamansa, amma daga bisani ya sake kai wasu munanan hare-hare Kananan Hukumomin Tsafe da Faskari da Kankara da ke jihohin Zamfara da Katsina.
Jim kadan da yin haka ne rundunar ’yan sandan Katsina ta sanya la’adar Naira miliyan biyar ga duk wanda ya kawo mata shi.
Tun daga lokacin ne ya yi ta kitsa hare-hare a yankunan Kananan Hukumomin da ke Tsafe da kuma Faskari a jihohin biyu.
Ko a baya gwamnatin Katsina ta sha shirya zaman sulhu tsakaninta da ‘yan bindiga amma alkawarin ba ya dorewa.
Idan za a iya tunawa Auwalu Daudawa a taba ajiye makamai tare da mika wuya ga gwamnatin Zamfara, inda ya yi alkawarin daina kai hare-hare, amma ya karya alkawarin da ya dauka ya sake daukar makamai.
Daudawa ya gamu da ajalinsa a ranar Juma’a a hannun abokan hamayyarsa a 2021.