An yi wa Shugaban ƙasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, Tiyatar Ƙwaƙwalwa a daren jiya Litinin don cire wani jinin dake cikin ƙwaƙwalwarsa da ya shafi faɗuwar da ya yi a gida a watan Oktoba.
Likitoci sun bayyana a yau cewa tiyatar ta yi nasara kuma Lula mai shekaru 79 yana “lafiya” kuma yana samun kulawa a cikin ɗakin kula da masu saurin mutuwa.
- Kebbi Da Brazil Zasu Yi Haɗin Gwuiwa Kan Sarrafa Nama Ta Hanyar Zamani
- Gobara Ta Ƙone Kayayyakin Biliyoyin Naira A Rumbun Ajiya Na NSIPA Da Ke Abuja
Likitoci sun bayyana cewa an yi tiyatar ba tare da wata matsala ba kuma Lula yana “ samun lafiya, ana duba shi” a ɗakin kula da masu saurin mutuwa, kamar yadda asibitin ya bayyana a cikin sanarwar da aka sanya a shafin Instagram na shugaban.
Lula ya yi MRI a Brasília bayan jin ciwon kai, wanda ya nuna cewa yana da jini a cikin kwakwalwarsa. Daga nan ne aka tafi da shi zuwa Sao Paulo don tiyata a asibitin Sirio Libanes.