Abba Ibrahim Wada" />

An Yi Wa Sir Ales Ferguson Tiyata A Kwakwalwarsa

Rahotanni daga kasar ingila sun bayyana cewa tsohon dan wasan Manchester United, Sir Aled Ferguson yana cikin wani hali na rashin lafiya wanda sai da takai anyi masa tiyata ta gaggawa a kwakwalwarsa a wani asibiti dake birnin Manchester.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ce dai ta bayyana labarin a shafinta na yanar gizo inda tace tana taya tsohon kociyan nata jaje kuma tana yimasa fatan murmurewa cikin gaggawa domin ya ci gaba da rayuwarsa.

Dangin tsohon mai koyarwar dai sun nemi kada labarin ya yada duniya saboda basason kowa yasan halin da yake ciki sai dai tuni labari ya yada duniya cewa dan kasar Scotland din yana sashen kula da marasa lafiya wadanda suke bukatar kula ta musamman a asibitin.

Tsohon dan wasan kungiyar, Cristiano Ronaldo ya bayyana jimaminsa da damuwarsa bisa rashin lafiyar tsohon mai gidan sa inda yace yana fatan zai warke kuma ya dawo da karfinsa.

Shima Dabid Beckham, tsohon dan wasan kungiyar, ya bayyana damuwarsa bisa labarin rashin lafiyar tsohon mai gidansa inda yace yana taya iyalansa jimamin halin da suke ciki na rashin tabbas kuma yana fatan zai warke cikin gaggawa.

Kungiyar kwallon kafa Liberpool, babbar abokiyar hamayyar Manchester United a kasar ingila ta fitar da sanarwar jimami da damuwa ga mai koyarwar inda tace tana taya kungiyar Manchester United da iyalansa jaje kuma tana fatan zai warke da wuri.

Sir Aled Ferguson dai ya shafe shekaru 27 yana koyar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United kuma ya lashe kofuna da dama a kungiyar.

 

Exit mobile version