Cibiyar kula da ayyuka ta Nijeriya (CIPMN), ta bayyana cewa ayyukan da aka yi watsi da su a Nijeriya a halin yanzu sun kai sama da na naira tiriliyan 17.
Magatakardan cibiyar CIPMN, Mista Henry Mbadiwe ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja a wani taron manema labarai.
- Tinubu Ya Amince Da Karin Albashi Da Kashi 300 Ga Alkalan Nijeriya
- Kwazon Kasar Sin A Ayyukan Shiga Tsakani Na Samun Yabo Daga Sassan Kasa Da Kasa
Mbadiwe ya yi nuni da cewa, binciken ya nuna cewa manyan abubuwan da ke haifar da ayyukan da aka yi watsi da su a Nijeriya sun hada da, “Rashin hangen nesa da rashin ingantaccen tsarin aikin daga farkon da rashin wadataccen kasafin kudin aikin da tsarin shari’a mara inganci da cin hanci da rashawa da hadin baki da kuma raunana cibiyoyi a Nijeriya wanda ke haifar da rashin ci gaba tare da sauye-sauye a harkokin siyasa.”
Ya tabbatar da cewa CIPMN za ta ci gaba da gudanar da sauye-sauyen gwamnatocin da suka shude da kuma gazawarsu tare da fara aiwatar da dokar da ta kafa cibiyar.
Ya ce, “Ba za mu iya ci gaba da zura ido ba muna kallon gwamnati tana barin irin wannan lamari ba.
“CIPMN za ta gudanar da canje-canjen gwamnatocin da suka gabata da inda suka samu rauni da kuma fara aiwatar sauye-sauye kamar yadda doka ta tanada.
“Za mu ci gaba da bin kadin dukkan ayyukan da aka fara aiwatarwa a Nijeriya, inda doka ta bukaci wadanda ke jagorantar wadannan ayyukan su kasance kwararrun manajojin ayyukan da CPMN ta ba su lasisi.”
Mbadiwe ya gargadi masu gudanar da ayyuka marasa lasisi a Nijeriya da su daina irin wannan aiki kai tsaye ko kuma su fuskanci sakamakon abin da suka aikatawa.
Ya ce, “Bari na bayyana muku cewa, cibiyar kula da gudanar da ayyuka ta Nijeriya ba za ta amince da manajojin ayyuka marasa lasisi suna kula da ayyuka a Nijeriya ba. Wadanda suke aikata hakan za su fuskanci mummunan hukunci.
“Dokar da ta kafa CIPMN ta bayyana cewa duk wanda ke cikin gwamnati da masu zaman kansu da ke shugabanta da jagorori da masu koyarwa fannin gudanar da ayyuka a Nijeriya dole ne a ba shi lasisin yin wannan sana’a.
“Ba shawara ba ce, doka ce, kuma muna tunanin lokaci ya yi da za mu fara bin doka a kasar nan.
“Daya daga cikin kalubalen da muke fuskanta a Nijeriya ba wai rashin dokoki ba ne, amma rashin mutunta wadannan dokoki ne, sau da yawa mutum zai aikata laifi kuma ya kauce wa hukunci.
“Duk da cewa ba mu da ikon kula da dukkan bangarorin, muna iya tabbatar muku da cewa a bangaren gudanar da ayyuka, mun himmatu wajen tabbatar da doka da oda, tare da tabbatar da cewa dukkan manajojin ayyukan suna da lasisi da kuma bin ka’idogin ayyukansu.”
Don haka, ya shawarci mutanen da suke da lasisin a fannin gudanar da ayyukan daga Cibiyar CIPMN da su tabbatar sun bi dokokin cibiyar yadda ya kamata.