Mataimakin gwamnan jihar, Mannir Yakubu, ya bayyana cewa, akalla gonaki 500 ne a fadin jihar manoma suka yi watsi da su domin tsira da rayukansu saboda yawan hare-haren ‘yan bindiga da suka jima suna addabar wasu sassan jihar.
A cewar Mannir, ayyukan ’yan bindiga sun janyo mummunar koma baya ga fannin aikin noma da ya hakan ya kai kusan sama da kashi 30 a cikin 100.
“Akalla gonaki 500 ne a fadin jihar manoma suka yi watsi da su domin tsira da rayukansu daga ‘yan bindiga, inda kuma hakan ya shafi gonakin guda 500 masu fadin kadada 58,000”.
Mataimakin gwamnan wanda kuma shi ne kwamishin ma’aikatar aikin noma ta jihar ya sanar da cewa, gwamnatin jihar na kokarin gain ta kara ragowar tan 1,000 da ke da shi.
Ya kara da cewa, jihar ta saba samun tan 30,000 na takin zama a duk shekara amma bara tan 10,000 kawai ta samu kuma dag abin da aka mata alkawarin ma tan 3,000 kawai suka samu.
“Mun saba samun tan 30,000 na takin zama a duk shekara amma a bara an samu tan 10,000 da aka yi mana alkawari, wanda daga cikin tan 3,000 kawai suka zo hannunmu.” In ji shi.