Hukumar kula da al’adun gargajiya ta kasar Sin ta bayyana cewa, gidajen tarihi na sassan kasar sun gudanar da bukukuwan nune-nunen kayayyaki 43,000, da tarurrukan ilimi 511,000.
An bayyana wadannan alkaluman ne a yau Lahadi a wani bikin tunawa da ranar gidajen tarihi ta duniya a gidan adana kayayyakin tarihi na babban mashigin ruwa wato Grand Canal a Beijing.
A cikin shekarar 2024, an yi rajistar sabbin gidajen tarihi 213 a kasar Sin, inda hakan ya kara yawan adadin gidajen tarihi na kasar zuwa 7,046, kamar yadda hukumar kula da su ta bayyana.
Kazalika, ta kara da cewa, kasar Sin tana kara fadada manufofinta na shiga gidajen tarihi ba tare da biyan kudi ba, inda sama da kashi 91 cikin dari na dukkan gidajen tarihinta ke ba da iznin shiga kyauta. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp