Abubakar Abba" />

An Zuba Jari Naira Biliyan 636 Na Kudin Fansho A Bankuna

Masu kula da asusun fansho sun zuba jarin naira biliyan 636.99 daga cikin jimlar kudin fasho a cikin bankunan da ake ajiyar kudadden na fansho a karashen watan Nuwambar 2018.
Wannan kashin na 7.49 masu kula da kudaden ne suke lura dasu. A bisa adadin da aka samo daga hukumar ta fansho ta kasa sun nuna cewar kudin sun kai jimlar naira tiriliyan 8.49.
an kuma zuba jarin kadarorin fanshoda suka kai yawan naira biliyan 15.7 ko kashi 0.19 da kuma naira biliyan 17.51 ko kashi 0.21 na kudinda aka zuba jarin akan kadarorin na fansho.
Shugaban kungiyar PFOAN ta kasa uwargida Aderonke Adedeji ta sanarda cewar, gudunmaar da kudin na fansho yake bayarwa akan tattalin arzikin kasa da ci gaba hakan ya janyo jan hankalin alummar gari.
Acewar uwargida Aderonke Adedeji rashin yin amfani da kudin tallafi na Paris Club da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi basu yi ba na basu biya giratutin ma’aikata tun a 2013 duk da sanya hannun yarjejeniya a tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin jihar Ogun, hakan ya haifar da matsala.
Ta yi nuni da cewar, a karo na farko Nijeriya zata iya yin tunkaho akan zuba kudi don zuba kudi akan yin ayyukan dogon zango.Uwargida Aderonke Adedeji ta yi kira akan ci gaba da sanya kaimi akan samar da kayan more rayuwa.
Ta kuma bayyana cewar hukumar PenCom tana shirin fara wanzar da shirin fansho na koyon sana’oin hannu gayan fansho dake kasar nan. A cikin sanarwar shirin zai janyo samada ma’aikata miliyan 20 a karkashin kudin da ake ajiyewa a asusun gata na shirin har naira tiriliyan uku.
Sanarwar ta kara da cewar, don a cimma burin shirin na hukumar ta PenCom an samar da tsarin fasaha.

Exit mobile version