• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ana Fargabar Wasu Leburori 3 Sun Mutu Sakamakon Ƙasa Ta Rufto Musu A Nasarawa

by Muhammad
2 years ago
Nasarawa

Ana fargabar wasu leburori uku da suke aikin hakar kasa a yammacin ranar Lahadin sun mutu bayan da wata kasa ta afko kansu a wani kauye da ake kira Unguwan Ayaba da ke karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa.

Ma’aikatan suna ta tono jar kasa tare da loda ta a cikin wata motar dakon kasa a wurin da suke hako kasar, sai kwatsam kasar ta yanko ta afka musu ta binne mutum hudu daga cikinsu.

  • Rikici Ya Ɓarke Bayan Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Sule A Gwamnan Nasarawa
  • Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Zaɓen Sule A Matsayin Gwamnan Nasarawa

An ce daya daga cikinsu an yi sa a ya tsallake rijiya da baya domin ya samu ya tsira daga karkashin kasar da ta danne su, sai dai ya samu raunuka yayin da sauran mutum ukun har yanzu ake kan tono ba a gansu ba.

Masu aikin ceto mutanen da mazauna kauyukan da suka hada da ‘yan uwan ​​wadanda abin ya shafa sun killace wurin domin tono gawarwakin ma’aikatan uku, sun fara aikin tonon tun da yammacin ranar Lahadi lokacin da abun ya faru, amma abin ya ci tura har zuwa lokacin kawo wannan rahoton.

Daya daga cikin masu aikin sa kai a wurin, Saliu Abdullahi, ya ce sun shafe fiye da sa’o’i biyu suna aikin tono ma’aikatan, ya kara da cewa ba za su bar wurin ba har sai sun hako gawarwakin ma’aikatan uku.

LABARAI MASU NASABA

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

Shima mataimakin shugaban kungiyar masu Tipper da ke karamar hukumar Keffi, Aminu Sunusi, ya ce sun aika da injin tona domin a samu a gaggauta aikin ceto mutanen.

Sunusi ya kara da cewa za su dauki kwararan matakai don kaucewa irin matsalar da ake ciki da dakile afkuwar irin wannan hadari a nan gaba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

November 8, 2025
Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi
Manyan Labarai

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

November 8, 2025
Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10
Manyan Labarai

Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

November 8, 2025
Next Post
AFCON 2023: Afirika Ta Kudu Ta Lallasa Ƙasar Namibiya Da Ci 4-0

AFCON 2023: Afirika Ta Kudu Ta Lallasa Ƙasar Namibiya Da Ci 4-0

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.