Cikin jawaban da suka gabatar yayin taron shekara-shekara na Boao dake gudana yanzu haka a birnin Boao na lardin Hainan dake kasar Sin, wasu jagororin kasashen waje sun yi kira ga sassan kasa da kasa da su hada karfi da karfe wajen tunkarar kalubalolin dake addabar duniya, tare da aiwatar da manufofin bunkasa tattalin arzikin duniya.
Yayin da yake tsokaci kan hakan, firaministan Singapore Lee Hsien Loong, ya yi maraba da kwazon kasar Sin a fannin ci gaba da bude kofofin tattalin arzikin ta ga duniya, yana mai fatan Sin din za ta ci gaba da goyon bayan cudanyar dukkanin sassan kasa da kasa, da hadin gwiwar shiyyoyi. Kaza lika ya yi fatan ganin samun karin gudummawar dukkanin sassa wajen ingiza bunkasuwar shiyyar da ma duniya baki daya, ta yadda hakan zai amfani nahiyar Asiya da ma sauran yankunan duniya.
A nasa bangare kuwa, firaministan Cote d’Ivoire Patrick Achi, cewa ya yi a wannan lokaci ne ma dandalin na Boao ya fi muhimmanci sama da kowane lokaci, duba da cewa kudurorin da aka amincewa ta hanyar hadin gwiwa, da goyon baya tsakanin sassan kasa da kasa yayin dandalin, na da kusanci matuka da burikan nahiyar Afirka da ma na daukacin bil adama.
Ita kuwa babbar daraktar asusun ba da lamuni na duniya IMF, Kristalina Georgieva, cewa ta yi hadin gwiwar sassan kasashen duniya ya riga ya haifar da sauye-sauye ga tattalin arzikin duniya, ta hanyar zurfafa hade kasuwanni, wanda hakan ya kara bunkasa kudaden shiga, da kyautata rayukan al’ummun duniya baki daya. Jami’ar ta ce “Duk da tasirin sassa masu fatan rarrabuwar kai, a yanzu mun san karfin mu ya karu bisa aiki da muke yi tare”.
Sannan mutane da dama daga kasashe daban daban, sun bayyana taron Boao a matsayin wani babban dandali na tattaunawa, wanda ya hada yanayin nahiyar Asiya tare da tasirin sauran sassan duniya. Fatan su shi ne al’ummun kasa da kasa za su rarraba basirar su, da abubuwan da suka amincewa tare, da hada karfi wajen tunkarar kalubalolin duniya karkashin wannan dandali.
An kuma gudanar da dandali mai taken “zamanantarwa irin ta kasar Sin”, wanda karamin dandali ne karkashin taron na Boao. Mahalarta dandalin sun bayyana yadda kasar Sin ke bin hanya mafi dacewa ta fuskar neman zamanantar da kasa, wanda baya ga taimakawa da hakan ya yi wajen wanzar da babban ci gaban kasar, a hannu guda ya kuma samarwa duniya wani sabon salon zamanantarwa, da raba dabarun hakan ga sauran sassan duniya, da kafa wani ginshiki na dinkewar duniya a nan gaba.
Yayin karamin taro mai lakabin “Zangon gaba na yanar gizo” kuwa, mahalarta zaman sun yi tattaunawa mai zurfi game da salon ci gaba da ake tunkara a zango na gaba na hidimar yanar gizo, da yadda za a iya gina fasahohin amfani da yanar gizo a nan gaba. (Saminu Alhassan)