Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta sanar da kama mutum 14 wadanda ta ke zargi da aikata fashi da makami da ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma aikata daba a farko makon watan azumin Ramadan.
Rundunar ta ce an samu nasarar kama mutanen ne a wani samamen da rundunarta ta dawo da zaman lafiya ta kaddamar.
- Boao: Kasar Sin Ta Karfafa Gwiwar Kasa Da Kasa
- Elon Musk Ya Zarce Barack Obama Yawan Mabiya A Twitter
Ta ce ta kuma kwato muggan makamai da haramtattun kwayoyi da kuma kayayyaki da aka sata.
A wata sanarwa da kakakin runduar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda ya ayyana yaki kan duk wani nau’i na aikin dabanci a fadin jihar.
‘Yan sandan sun ce suna iyakar kokarinsu wajen dakile dukkan ayyukan bata-gari a jihar.
CP Mamman Dauda, ya gargaÉ—ldi duk masu aikata laifi da su guji yin hakan saboda za su iya fuskantar hukunci mai tsanani idan aka kama su.
Ya kuma bukaci al’umma da su kai rahoton duk wani abu da ba su yadda da shi ba, su kuma guji daukar doka a hannunsu.