Duniya ta kasa kunne ta ji sakamakon tattaunawar da shugabannin tattalin arziki biyu mafi girma a duniya wato shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden suka yi, a gefen taron kolin kungiyar APEC da ya gudana a ranar 15 ga watan Nuwamba. Shugabannin biyu sun shafe sama da sa’o’i hudu suna tattaunawa kan batutuwan da za su daidaita dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, wanda a bayyane ta kasance alakar diflomasiyya mafi muhimmanci a duniya a yau.
An samu kyakkyawar fahimtar juna a tattaunawar. Bangarorin biyu sun sanar da samun ci gaba a fannonin da Amurka ta dade take son kara yin hadin gwiwa da kasar Sin, ciki har da batun samar da sinadarin fentanyl a kasar Sin, gami da sake dawo da tattaunawar soja tsakanin kasashen biyu, wani bangaren da Amurka ke son a tabbatar da cewa an kauce wa rashin fahimtar juna da rikidewa zuwa rikicin soja.
- Shugaban Kasar Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Faransa
- Xi Da Putin Sun Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Tattaunawa Tsakanin Manyan Jami’yyun Siyasar Sin Da Rasha
Bangarorin biyu sun fuskanci juna da nufin nuna wa duniya cewa a shirye suke su daidaita dangantakarsu cikin gaskiya. Don haka, kowanensu na cike da kwarin gwiwa wajen bayyana gaskiya da adalci da ci gaba. Kuma hakan ba shakka ya ginu ne bisa sakamakon taron Bali na bara, da kuma goyon bayan ci gaba da harkokin diflomasiyyar da suka gudana a baya-bayan nan, da daidaita matakan aiki kan wasu muhimman batutuwan da suka ambata.
Shugaba Xi, a jawabinsa na bude taron, ya jaddada cewa, duniya na da girmar da kowace kasa za ta gudanar da harkokinta ba tare da kawo tsaiko ga wata kasa ba, kana, nasarar da wata kasa ta samu dama ce ga wata kasa daban, yayin da shugaba Biden shi kuma ya bayyana muhimmancin tabbatar da cewa gasa ba ta nufin rikici.
A ra’ayi na, tattaunawa da sadarwa su ne mabudin cimma daidaiton da ya dace. Matukar za mu iya sarrafa rashin jituwar dake tsakaninmu ta hanyar tattaunawa da sadarwa da kuma fahimtar juna, ina ganin akwai damar nunawa jama’a da duniya cewa za a iya tafiyar da dangantakar wadannan kasashen biyu cikin gaskiya da adalci. Yana da matukar muhimmanci ga bangarorin biyu su mayar da martani ga bukatun duniya ta hanyar mutunta alakar dake tsakaninsu.
Duniya a halin yanzu tana fama da ainihin rikice-rikice da dama, kama daga rikicin sauyin yanayi da rashin tabbacin tattalin arziki, zuwa rikice-rikicen dake tasowa na rashin wadatar abinci a dalilin rashin tsaro. Wadannan su ne tarin matsalolin da duniya ke fuskanta da ya kamata a warware a cikin wannan karni na 21, kuma zaman lafiya da jituwa tsakanin Amurka da Sin ka iya zama silar daidaituwar wadannan matsaloli.
Kasashen duniya ba sa so a bar su da zabi tsakanin Amurka da Sin. Duniyar da aka gina a kan bangaranci da rarrabuwar kawuna inda Amurka ke jagorantar wani bangare yayin da Sin ke jan ragamar wani bangare ba shi da amfani ga kasashen duniya. Kuma ba zai taimaka wajen warware matsalolin da duniya ke ciki ba. (Muhammed Yahaya)