Yanzu haka tawagar gwamnatin tarayya da shugabannin ƙungiyar malaman Jazdmi’o’i (ASUU) na wata ganawar sirri domin tunkarar rikicin da ke faruwa da kuma kaucewa yajin aikin ƙungiyar. Taron wanda aka fara da misalin karfe 4:30 na yammacin yau Laraba yana gudana ne a ofishin ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman. Karamin Ministan Ilimi, Dakta Yusuf Sununu, da wasu manyan jami’an ma’aikatar na cikin tawagar gwamnatin tarayya.
Shugaban ƙungiyar ASUU, Emmanuel Osodeke, wanda ke jagoranci tawagar ƙungiyar, ya bayyana cewa taron na da nufin tattauna batutuwan da suka shafi jami’o’in da kuma hana shiga yajin aikin da aka shirya gudanarwa.
- Matsalolin Ilimi A Nijeriya Da Hanyoyin Gyara Su (2)
- Sharhin Littafin Zube Na ‘Sidi Ya Shiga Makaranta’ Na Umaru Ladan Da Michael Crowder (4)
Osodeke ya bayyana fatan cewa taron zai warware waɗannan matsaloli, tare da burin cika alkawuran da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi, ta yadda za a kaucewa kawo cikas a harkokin jami’o’in.
Farfesa Tahir Mamman ya jaddada cewa taron wata dama ce da ɓangarorin biyu za su tattauna don magance matsalolin da suka shafi jami’o’in. Ya ce a baya ASUU ta sanar da ma’aikatar al’amura da dama, wanda hakan ya sa aka cimma matsaya domin hana ƙungiyar ci gaba da yajin aikin da take yi.
ASUU dai ta yi gargadin shiga yajin aikin gama gari sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatun ta. Osodeke ya buƙaci gwamnati da ta magance duk wasu matsalolin da ke faruwa a cikin makonni biyu don gujewa matakin da zasu ɗauka.